Zaɓen 2027: ADC ta fitar da sharuɗan tsayawa takara a inuwarta
Jam’iyyar ADC a Najeriya, ta bayyana muhimman abubuwan da ta ke buƙata ɗan takara ya mallaka kafin tsayawa takara a ƙarƙashin inuwarta a zaɓen da ke tafe na 2027.
Da yake jawabi yayin taron kwamitin ƙoli na ADC da ya gudana ranar Talata a Abuja babban birnin Najeriya, shugaban Jam’iyyar na ƙasa Sanata David Mark, ya ce jam'iyyar za ta tsayar da ƴan takarar ne waɗanda suka cika wasu ƙa'idoji huɗu; da suka haɗar da kyakkyawan hali, ƙwarewa a fannin shugabanci, da ƙwarin gwiwa, da kuma kasancewa mai ɗa’a.
Ana kyautata zaton tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar, jigo a ADC ɗin, wanda ke da ra'ayin haɗin gwiwa tun lokacin da ya sha kaye a matsayin ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, zai sake tsayawa takarar shugabancin ƙasa a ADC bayan yunƙurin zama shugaban Najeriya da ya yi a baya.
Ana kallon goyon bayan Atiku na shiga ƙawancen a matsayin wani yunƙuri na jagorantar haɗin gwiwar wanda ke fatan shafe tarihin jam'iyya mai mulkin ƙasar wato APC a zaɓen 2027.
Haka kuma ana ta raɗe-raɗin cewa shima tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ka iya fitowa a matsayin ɗan takara a cikin ƙawancen, saboda alaƙarsa ta ƙut da ƙut da wasu magoya bayan jam’iyyar ADC ɗin waɗanda ke ɓangaren kudanci da arewacin ƙasar.
Amma duk da jita-jitar da ake ta yi game da fitowar Jonathan ɗin takara a Jam’iyyar ADC, har yanzu bai bayyana wani bayani a game da batun ba.
Sai dai ziyarar da tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan, ya kai wa shugabaan jam’iyyar ADC Sanata David Mark, a makon jiya ta sake haifar da cece-kuce game da ƙarfafa zargin tsayawar tasa, ko da yake a wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar Malam Bolaji Abdullahi, ya fitar a baya-bayan nan, ya ce ziyarar ba ta da alaƙa da siyasa, inda ya bayyana ta a matsayin ta kai da kai.
Su dai masu tsinkaye kan lamuran siyasa, na ganin akwai yiwuwar nuna sha’awar tsayawa takara a ziyarar da tsohon shugaban ƙasar ya kai wa David Mark, a gidansa na Abuja, wanda ya kasance shugaban majalisar dattawan ƙasar a zamaninsa, wato tsakanin 2010 zuwa 2015.
A halin da ake ciki, tuni ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi sun nuna sha'awarsu ta tsayawa takara a inuwar jam’iyyar ADC, har ma sun yi alƙawarin yin wa'adi ɗai-ɗai kawai a ƙarkashin tsarin karɓa-karɓa tsakanin yankin Arewaci da Kudanci.
managarciya