Atiku ya aiyana ranar da zai shiga ADC

Atiku ya aiyana ranar da zai shiga ADC

 
Tsohon mataimakin shugan kasa Alhaji Atiku Abubakar ya sanar da mutanen jihar Adamawa da Nijeriya baki daya zai shiga jam'iyar ADC a ranar Litinin.
Atiku a wani jawabi da ya yi ga magoya bayansa a Yola ya ce sabuwar tafiya ta kai mu jam'iyar ADC a gobe shugaban jam'iya zai yanka min katin shaiga cikin jam'iyar ADC.
Shiga jam'iyar na nuni da cewa harkokin siyasa na 2027 din a tafiyar Atiku zai soma daga Litinin kenan domin ya yi matsaya kan tafiyar siyasar da zai yi a 2027.