Ana jiran bayanin daga Gwamnatin Sokoto kan harin Amerika 

Ana jiran bayanin daga Gwamnatin Sokoto kan harin Amerika 
Sojojin Amurka sun kaddamar da wani mummunan hari kan wuraren ‘yan ta’addan kungiyar ISIS a Najeriya a ranar Alhamis.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, kusan wata guda bayan ya yi barazanar kai hari kan Najeriya bisa zargin barin ‘yan ta’adda su rika kai hare-hare kan Kiristoci.
A wani sakon da ya wallafa a shafin Truth Social, Trump ya ce:
“Da daren yau, bisa umarnina a matsayina na Babban Kwamandan Rundunar Sojoji, Amurka ta kaddamar da wani gagarumin hari mai tsanani kan ‘yan ta’addar ISIS a Arewa maso Yammacin Najeriya, wadanda ke kai hari tare da kashe mutane cikin mugunta, musamman Kiristoci marasa laifi, a matakin da ba a taba ganin irinsa ba tsawon shekaru da dama, har ma da ƙarni!”
Harin da aka kai a garin Jabo a ƙaramar hukumar Tambuwal ya haifar da fargaba a cikin al'umma tare da shakkun shin 'yan ta'adda ne ake hari ko mutanen gari.
Sai dai a yanzu ana jiran bayani daga gwamnatin jiha kan lamarin wanda hakan zai samar da haske da sahihin ya bayani kan harin domin hankalin mutane ya kwanta a yankin Arewa ta yamma.