Oktoba: Zanga Zanga Ta Barke ana Tsaka da Bikin Ranar 'Yanci 

Oktoba: Zanga Zanga Ta Barke ana Tsaka da Bikin Ranar 'Yanci 

Matasan Najeriya sun fito kan tituna domin fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa. 

A birnin tarayya Abuja, matasan sun fito dauke da alluna da suke kira ga gwamnatin tarayya kan kawar da zalunci a tsarin shugabanci.
Legit ta gano yadda zanga zangar ke gudana ne a cikin wani bidiyo da tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore ya wallafa a Facebook. 
Legit ta ruwaito cewa masu zanga zangar tsadar rayuwa sun gabatar da bukatu 17 ga gwamnatin tarayya. Matasan sun bayyana cewa idan ba a biya musu bukatunsu ba za su cigaba da yin zanga-zanga a fadin ƙasar nan. 
Matasan Najeriya sun fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa karo na biyu a birnin tarayya Abuja. 
A cikin wani bidiyo, matasan suna yawo ka kam titi ne suna cewa yunwa suke ji saboda haka a dauki mataki. 
Daga cikin abin da masu zanga zangar ke cewa kawai buƙatar inganta Ilimi da kawo saukin rayuwa.