Majalisar zartarwa ta amince da  Kasafin kuɗi na 2026 a Sokoto

Majalisar zartarwa ta amince da  Kasafin kuɗi na 2026 a Sokoto

Majalisar zartarwa ta aminta da kasafin kudin na 2026 a Sokoto  za a gabatar da shi gaban majalisar dokoki ta jiha.
Kwamishinan kasafi a jiha Abubakar Zayyana ya sanar da hakan bayan kammala zaman majalisa a satin da ya gabata ya ce majalisa ta aminta da daftarin kuma za a mika shi a zauren majalisar dokokin jiha.
Ya ce in daftarin kasafin  ya fita aka tabbatar da shi a gaban majalisa mutane za su tabbatar da Gwamna mai son cigaba ne.
Haka ma Kwamishinan yada labarai na jiha Sambo Bello Danchadi shi ma ya bayyana za a sake  ginawa da gyara wurin gudanar da aiki a ma'aikar jindadin alhazai ta jiha kan kudi sama da miliyan 469.
Saboda ma'aikatar tana fama da rashin wuraren aiki, za a yi aikin ne cikin wata shida.