ANA BARIN HALAL...:Fita Ta 48

ANA BARIN HALAL...:Fita Ta 48

ANA BARIN HALAL...:

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* 

*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin Ƙarfe

Burin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*

https://chat.whatsapp.com/BD1UrswOFvN0CTIfsg30JL?mode=ems_copy_c
*Page 48*


*********
Yana fita kuwa ta sauƙe ajiyan zuciya mai ɗan ƙarfi, nidai kawai kasa sakewa nayi da ita, ita dai sai ɗan jana da hira takeyi nakasa sakewa, ana ƙiran  sallah kuwa ta wuce ɗakinta, amma sai da tagaya  mun, ina tuƙa tuwa kuwa ya shigo kitchen ɗin, ɗan hararan shi nayi na juyi na cigaba da tuƙawa,  haɓan shi ya ɗaura a kafaɗa na bayan ya saka dukka hannayen shi akan kunkumi na,  "beauty zanje nayi sallah",   dakatawa nayi da tuƙin nace,  "A.G nah ya kamata ka iya gayawa mummy wannan zance? Tou yanzu idan ta tambayeni mai zan iya cewa"?  Dariya yayi mai ɗan sauti kaɗan,  "ki ƙirani zan mata bayani, don ni kam a hargitse nake, ina buƙatar matata",    dakatawa nayi da abunda nakeyi cike da mamakin shi nace,  "don Allah ka wuce masallacin kada mummy ta shigo",    "alwalan ne baby ya lalace" aiko ji nayi kaman na nutse a wurin, gaskiya ashe A.G bai da ta ido, Allah ya taimakeni sai naji muryan Daddy yana neman shi, da sauri ya fice a kitchen ɗin, ajiyan zuciya na sauƙe, na furta "Allah ka taimakeni har mu bar gidan nan kada A.G ya sake kunyata ni, ni dama ashe haka yake ne"? Na faɗa wa kaina da kaina, ina gamawa na wuce ɗakin Heedayah lokacin mummy ta tashe ta tayi sallah, tana yamutsa fuska irin an tashe ta tawuce toilet tayi alwala, bayan tayi sallah ne tace mun zataci abinci sai muje gidan su goggo,  haka ko akayi suna gama cin abincin muka wuce gidan Goggo, na ɗauka mummy zata mun magana sai naga bata ce komai ba, gidan Dadda mukaje aka gaisa, mun kai good 1hr a gidan muna hira, godiya sosai Alhaji da Dadda suka mana da zamu tafi, suka mana addu'a sosai, gidan Goggo muka shiga da chan, mun samu goggon kwance babu lafiya, mura da zazzaɓi ne ke damunta, haka muka zauna a parlonta, godiyan sinasir ita ma tayi mun sosai, daga baya ta mana nasiha na zaman lafiya sosai, anan take gayawa M.G mai aikin gidan Alƙali zuwan ta biyu tana so taje gidan shi taga matar shi ta mishi murna, dariya yayi yake gayawa Goggon ya sayi wani ƙaramin gida nan kusa da su na wasu magada ɗaki biyu ne a ciki sai ɗakin girki da ƙaramin store, zai bata ta koma ciki insha Allahu,  albarka sosai goggo ta saka mishi, "Aunty nice idan baki manta matar ba, itace wacce ta zabgawa M.G itace a bayan shi Lokacin da yaje gidan alƙali yin waya yana yaro",  jijjiga kai nayi alaman na tuna labarin matan, ana sallan la'asaar A.G ya ɗauke ni muka wuce gidan mu, har parlorn ummie ya shiga suka gaisa, ya daɗe zaune a parlon tunda Abba baya nan, hajiya ummah bata nan sunje gaisuwan rasuwa itada Aunty Rakiya da Mamah chan garin su Abba, bayan ya tafi ne nida hafsy muka  je na duba jikin sabeer a chan side ɗin mamie, tunda muka shiga take wani bina da kallo daga sama har ƙasa, gaisheta mukayi na duba jikin sabeer da yake bacci,  Allah sarki duk ya zabge har abun tausayi, ganin irin kallon da take bina da shi yasa hafsy tace,  "Adda muje ko",  hararanta mamie tayi ƙasa-ƙasa, muna dab da zamu fice najiyo muryanta tana,  " Ayshaa auren sati biyun ne ya wani zabgar da ke haka? Ko baya baki irin abinda ake baki a gida? Ko yafi ƙarfin kine a auratayyah duk ya figar da ke haka"? Nidai murmushi nayi bance mata komai ba, ganin bazanyi magana ba yasaka ta ja tsaki tace,  "tou Allah ya rufa asiri, hala a jininku ne keda habiba rashin dace da aure",  "ajinin habiba dai, Adda kam ae banga wanda yakaita dace da miji ba a gidan nan, sai dai muce Allah yasaka a madadin su, miji ya ganka yana sonka kam ae duniya ne, idan har ba tura mishi kai akayi ba kam ae kayi dace babba"  habiba ta faɗa tana riƙo hannu na muka fita, ina jin mamie na aika mata da zagi, amma ko ajikinta har muka fita ina mamakin halin hafsy na rashin barin sai ta kwana.

Ɗakin ummie dukan mu muka ƙule, daɗi nakeji kaman zanyi yayah, sai ina ganin gidan ya dawo mun sabo, sai shiri ummie take mun na kayan marmari kaman ba kwanan nan tagama na auren ba, har kilishi ta saka aka mana, ga dambun kaji da ta saka aka sake mana, daga ni har su yayah ta haɗa mana kaya rigijib, hira sosai mukeyi har aka ƙira sallan magrib, anan hafsy tace na shiga nayi alwala,  "bana sallah hafsy"   kallo ta bini da shi cike da mamaki, chan tace "wani irin baki sallah Adda? Yaushe naje gidan ki nasamu bakiyi? Sau uku kikeyi wannan watan kenan"?
Girgiza kai nayi ba tare da nufin komai a raina ba nace,  "tun wancan bai ɗauke ba, kusan 2weeks fah? Har tsoro nakeji kada jinina ya ƙare",  na faɗa ina maida kaina kan ummie da ta shigo lokacin,  "ummie kiji wai Adda mensis ɗinta 2weeks bai tsaya ba amma take zaune bata ce wa Yayah A.G suje asibiti ba, sai jininta ya ƙare mu shiga uku",  ta faɗa tana wani harara na kamar nice ƙanwar ita kuma yayar.

Kallona ummie takeyi cike da mamaki, "tun yaushe kika fara sokancin ɓoye mun abu irin haka eyyeh ayshaa"? Ummie ta tambaye ni,   "ummie wallahi na ɗauka zau ɗauke danaga ya rage zuwa, amma kullum sai naga akwai yananan, ni ummie tsoron aje asibiti ace wani allura za'a mun nakeji",  kallona ta tsaya tanayi, chan kuma sai tace "hafsy tashi kije kiyi sallan", tashi hafsy tayi ta fice, sannan ummie kuma ta mayar da duban ta kaina,  "yanzu shi A.Gn bai ce miki komai ba? Tun angama bikin ku da kwana nawa ya dawo miki"? Ummie ta faɗa, tura baki nayi gaba saboda nasan yanzu za'ace asibiti,  "ummie ni baice komai ba, amma yau da mukaje gidan su naji yana gayawa mummy, inaga tunda tsohuwar ma'aikaciyar asibiti ce zata san yadda za'ayi",  ummie ni tun ranan da aka kaini yazo mun, yau kusan 15dys ko 16 ne ma" na faɗa ina duban ummin.
  Shiru ummie tayi tana kallona, sallaya riƙe a hannunta,  "Ayshaa ni wallahi ban san ina zaki kai rashim wayo ba, ae komai kiga baki gane ba sai ki ƙira ki gaya mun, Allah ya rufa asiri, bari muji me ita mummyn zatace tukun, idan abun bai yiwuba sai ki daure kuje asibiti kicire tsoron nan",  kaman an taɓo mun abunda yake damuna,  "ummie ni tsoron gidan ma nakeji, kinsan abubuwan da nake gani kuwa a gidan"?  Ƙawai nasamu bakina da gayawa ummie duk abubuwan da suke faruwa, ido ta zare tana kallona, chan tace,  "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, shine kuma da ga ke har A.Gn baku gayawa kowa ba? Tou ae wannan kam akwai matsala babba a gidan, hala ma wani matattaran shaiɗanu akaje akayi ginin shine suke damun ku? Gaskiya wannan ba abun da za'ayi shiru bane, bari nayi sallah na ƙira mummyn shin, ae sai suje su sauƙar miki da jininma suce kunzo musu gidan su, gara ayi sauƙan qur'ani kafin abun yayi yawa",  tana gama maganan ta fara sallah.


Shiru nayi ina tunanin abubuwan daya faffaru a gidan, ko dai aljanu ne a gidan na faɗa a zuciyata, sai naji zuciyata ya yanke lokaci ɗaya, kada fa sune suka shiga jikina har nake jin abunda nakeji akan A.G? Hankali na nane naji duk ya tashi, a haka hafsy ta shigo ta sameni,  "Adda kinyi azkhar ne? Naga kinyi shiru kina tunani"? Lokaci ɗaya sai naji hankali na ya ƙara tashi, tunda naje gida na kuwa nayi azkhar ko karatun qur'ani? Hala ko addu'a idan zan kwanta ma na manta ranan da nayi, ko alwala idan zan kwanta kuwa inayi? Sai naji ƙwaƙwalwata ta kasa tuna inayi kp banayi, sai kawai nabar tunanin na fara azkhar ɗin da hafsy ta tuna mun, ima idar wa na karanta surutul mulk.

Ummie tana idar wa ta juyo kaina,  "aysha kima addu'a kuwa"?   Shiru nayi kaman zanyi kuka na ƙura mata ido,  "hmm Allah ya kyauta, hala daga ke har A.G ɗin kunje kuma wasa da addu'a",  nidai bance mata komai ba, wayanta ta ɗauka ta ƙira mummy, ina jin su suka fara magana akan matsalan da nagayawa ummie, nan itama mummy take mata bayanin ae tun ɗazu da A.G ya mata maganan period ɗin ta samu sister ta sukayi magana, suma dama sunyi tunanin ko jinnu ne, don bayan A.G ya kawo ni daya koma ta ajiye shi sunyi magana sosai, inda duk abunda yake faruwa sai da ya gaya mata, nan Mummy tace tou zata samu Daddy ta gaya mishi A.G ya wuce aikin shi chan Abuja shi kaɗai, ni ka abarni a bauchi a gwada magani agani, itama Ummie tace yanzu kuwa zata gayawa Abba, duk yadda ake ciki zuwa safiya zataji ta, bayan sunyi sallama ne ummie ta titsiyeni da wasu abubuwan da mummy ta gaya mata, kawai sai naji kuka yazomun, kuka na ringayi ummie na mamakina, chan dai ta rabu dani ta ƙira Abba ta gaya mishi,  amma Abba sai yace wai babu matsala idan anyi hakan, amma ba shi ko ummie bane suke da hurumin nema mun magani, saboda gudun zargi ta barni a gida na ko wurin surukuwata suyi mana magani, don shi Abba cewa yayi ƴat'shi lafiyanta qalau sai dai matsalan daga A.G ne, amma kafin ayi komai shi yafi so muje asibiti akan issue ɗin jinin,  haka dai ummie ta rabu da shi don tasan halinshi, ba lallai bane dama ya yadda da maganan wasu iskokai,  sai wurin 9:00pm A.G yazo ɗaukana, aikuwa ummie ta haɗamu ta mana kacha-kacha akan addu'a, da kuma zama da alwala, kanshi kuwa ya sunkuyar yana ta bada haƙuri, domin ta nuna mishi dole amatsayin shi ma namiji kuma babba ya dinga hankaltar da ni,  har mota hafsy ta rakamu, naso maje naga sabeer, amma ummie ta nuna mun hanyar waje, haka na wuce hafsy tana dariya don ita ta kitsa komai.

A mota babu wanda yace komai daga no har A.G duk munyi shiru,  a haka muka tsaya ya sayi Bread da nama sai yougouth muka shige gida,  a parlor ya zauna ya ƙura mun ido,  "Eeshan A.G kin san ni duk mummy ta razanani da gidan nan? Kinsan nifa mutum baya bani tsoro, don ko ɓarawo ne sai muyi gaba da gaba da shi banji tsoro ba, amma aljani? Gaskiya  ina tsoro,"  ya faɗa yana nuna mun ledan naman wai na ɗauko filet da cups muci, kallon shi nayi baki a buɗe nace,  "ni kaɗai zanje kitchen ɗin? Gaskiya ni tsoro nakeji, kawai kazo muje tare",  ido ya ƙwalo mun yace,  "me zai sameki? Ga wuta ga komai,  jeki nima ae dare nake tsoro ba wai yanzu ido naganin ido ba,"  zama nayi ina kallon shi, ganin da gaske yake bazai rakani ba,   "A.G na bazaka raka Eeshan kaba"? Na faɗa ina rausayar da kaina,  miƙewa yayi yace,   "wuce muje kin cika tsoro,"  bayan mun ɗauko na zuba mana tare babu yadda na iya, don ni wallahi kunyar cin abincin tare da shi nakeyi, amma yadda ya takura ni haka nake daurewa nake ci,  "ina ga gobe tafiyan nan ba zai  yiwu damu ba beauty".

Don Allah kuyi hƙr bani jin daɗin jikina

*AUNTY NICE*