Adam A Zango ya auri wata:yar Fim a asirce
Fitaccen jarumin masana’antar fina-finan Hausa, Kannywood, Adam A. Zango ya agwance da jaruma Maimuna Musa, wadda aka fi sani da Salamatu a shirin Garwashi
Marubuciya a masana’antar, Fa’iziyya D. Sulaiman ce ta sanar da auren nasu a wani rubutu da ta wallafa a Facebook
Auren dai ya zo cikin bazata, domin babu wanda ya san da neman sai labari aka ji jaruman sun shiga daga ciki.
Jaruma Maimuna matashiya ce wadda tauraronta ya fara haskawa a Kannywood.
Ta yi fina-finai kamar Kwana Casa’in, Garwashi da sauransu.
A baya-bayan nan ma fitacciyar jaruma a masana’antar, Rahama Sadau, ita ma ta yi aure, lamarin da ya bai wa mutane da dama mamaki.
managarciya