Kotu a Zamfara Ta Baiwa Kwamishinan Gona Wa'adin Kwana Biyu  Ya Dawo Da Tarakta 58 

Kotu a Zamfara Ta Baiwa Kwamishinan Gona Wa'adin Kwana Biyu  Ya Dawo Da Tarakta 58 
 
Daga Hussaini Ibrahim.
 
Babbar Kotun daukaka Kara ta biyu ta jihar Zamfara,wace Mai shaari'a Bello Shinkafi ke jagoranci ya ba Kwamishinan Ma'aikatar Gona wa'din   Kwana biyu da ya dawo da Taraktoci 58, da  ake zargin ya  batar. 
A kawo su gaban kotu dan biyan Kamfanin Dunbulun Investment hakin sa da ya ke bin Gwamnatin Jihar ta Zamfara.
 
 Barista Musbahu Salahudini wanda ya ke kare Kwamfamin Dunbulum, yayi wa manema labarai karin bayani akan hukuncin Kotun kamar haka, a shekara ta  2019,Kotun daukaka Kara ta Uku  ta yi hukuncin tsakanin Gwamnatin Jihar Zamfara za ta biya Kamfanin Dunbulun Investment kudi naira miliyan Dari biyu da Sharin, alokacin Gwamnatin ta biya miliyan Dari da 'yan Kai saura miliyan Dari da uku suka rage bata biya ba, sai babbar Kotun ta uku ta ba da Umarni kama kaddarorin Gwamnatin a lokacin, ta kama wasu motocin Gwamnatin da Taraktoci Ma'aikatar Gona 58, a cikin watan Disanba na bara da nifin a yi gwanjan motocin dan abiya Kamfanin Dunbulun kidin sa sai Kotun ta yi ta jan-kafa, kan batun saida kaddarorin.Inji Barista Musbahu.
 
Barista Musbahu ya Kara da cewa, Dokar taba Mai Kara dama in baka gamsu da mai shari' ba ka kara ga Kotun gaba wannan ne ya ba mu damar kai karar, a Kutun daukaka kara ta biyu, dan neman  hakinmu.
 Mun shigar da kara  Kotun ne dan tilastawa Kuto ta yi gwanjan kayan Dan biyan mu hakokin mu sai muka samu labarin cewa, kwamishinan gona ya kwashe Taraktocin 58 ya saida, mun shedawa Mai shari'a  Kotun daukaka Kara ta biyu agaban Lauyan Gwamnati.
 Mai shaari'a Bello Shinkafi ya amsa kokenmu ya ce Kwamishinan Gona da ya gaggauta kawo Taraktoci 58, cikin kwana biyu kuma ya mika kansa a gaban Kotun a ranar 14/9/2022, ya kare kansa akan wasa da shiri'a da yayi, Motoci na gaban  Kotun ya zai kwashe ya sayar.inji  Barista Musbahu Salahudini.
 
Manema labarai sun nemi jin tabakin  Lauyan Gwamnati Jihar Zamfara,ya bayyana masu cewa, bai da hurimin yin magana  sai da Umarni Kwamishinan shari'a na Jihar.