Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 14,940 a Sakkwato

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 14,940 a Sakkwato

 

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 14,940 a jihar Sakkwato kamar yadda gwamnatin jiha ta sanar.

Shugabaan kwamitin kula da ambaliyar ruwa  ta jiha Muhammad Bello Idris ya sanar da hakan a lokacin da yake gabatar da rahoton kwamiti ga gwamnan jiha Ahmad Aliyu a ranar Litinin ya ce kauyukka 1,341 a kananan hukumomi 22 ne lamarin ya shafa a wannan shekarar.
Ya ce Gonaki 11,390 ne suka lalace amfanin gonar ma haka.
Kwamitin a rahotonsa ya yi kira ga gwamnati ta ba da agajin gaggawa ga wanda lamarin ya shafa.
Gwamnan ya godewa kwamitin tare da ba su tabbacin aiwatar da rahoton kwamitin a tsanake.