Marubuci Mutum Ne Mai Kawo Cigaba Da Gyara A Cikin Al'umma---Mai Ƙosai

Marubuci Mutum Ne Mai Kawo Cigaba Da Gyara A Cikin Al'umma---Mai Ƙosai
Mai karatu Assalamu Alaikum. Barkanmu da yau, Sannunmu da kasancewa da kai a wannan filin na TAURARUWARMU A YAU.
 
Shiri ne da ke gayyato marubuta domin a zanta da su, don jin nasara da kuma ƙalubalen da ke Cikin rubutu dama duniyar marubuta. A wannan  mun samu nasarar zantawa da ɗaya daga cikin fitattun marubuta a Arewa. 
Ga  yadda firar ta mu  ta kasance da marubuciyar.
 
Daga DOCTOR MARYAMAH 
 
 
Da farko za mu so mu ji cikakken sunan Tauraruwar ta mu.
Sunana Maryam Abdul'aziz wadda aka fi sani da Mai Ƙosai a social media da ma wajenta.
 
Mai ƙosai, ƙosai ake siyarwa ko kuwa soyayyar da ake yiwa ƙosai ce?
 
Ko ɗaya dai gaskiya cikin biyun, na samo aslin ƙosan ne kawai saboda tsokanar wata ƙawata dan nace mata ina son na ci ƙosai da burudi yafi min daɗi, shi kenan ta saka min mai ƙosai ni kuma na rataya a wuyana, nake kuma amsa sunan mai ƙosai. Duk da dai yanzu ina son shi.
 
Ki kace, kina son abincin mutanenmu, ma su sanya mu nishaɗi kenan. Lox.
 
Eh gaskiya ina so
 
Ko za mu iya jin ɗan taƙaitaccen tarihin rayuwarki?
 
Kamar yadda na ce suna na Maryam Abdul'aziz, an haifr ni a jihar Kano, na yi karatun fimare da sikandire na duk a jihata, bayan na kammala na wuce makarantar gaba da sikandire inda na yi N.C.E yanzu haka na kammala karatuna.
 
Maryam tana da aure, idan da aure yara nawa?
 
Ina da aure, yara babu
Kwatsam! Ga ki a duniyar rubutu da marubuta. Ta ya aka tsinci kai a wannan duniyar?
 
To ni dai zan iya cewa kawai na ganni a duniyar Marubuta ne, saboda soyayyata ga Rubutu da Marubuta
ina burin   naga na zama Marubuciya, sai kuma ga shi Allah ya nufa na zama.
 
Kawai kina ra'ayin rubutu sai ki ka tsinci kanki a duniyar rubutu da marubuta, ta ya kenan? Kin fara rubutun ne a wayarki ta hannu ne, ko kuwa a paper ki ka fara rubutawa kina nunawa al'umma cewa kin fara rubutu? Ko ya abin ya ke?
 
Na tsinci kaina a duniyar Marubuta ta hanyar fara rubutu a takarda tun 2010 na fara rubuta wani labarina mai taken *RAYUWAR AISHA* a littafi, inda a gida ganin cewar ko ƙaramar sikandire ban gama ba nake rubutu aka hanani, a cwwar Mamanmu zai raba min hankalina gida biyu, na kasa tsaida hankalina kan karatu, hakan ya sa na tattara na watsar, bayan nan kuma ina SS2 shi ma na sake rubuta wani a littafi sai dai na mance sunansa, na sami mutane da dama sun karanta labaran biyu, daga nan na ajjiye komai har sai da na kammala sikandire na dawo gida na an bani damar riƙe babbar waya sai naga ana rubutu ta waya, sai kawai nace ni ma bari na fara rubutuna ta nan, cikin ikon Allah dana fara sai kuma rubutuna ya sami karɓuwa har ta kai yanzu ni ma an san ni a duniyar Marubuta.
 
Ma sha Allah. Mai ƙosai ko tana da uwar ɗaki a duniyar rubutu?
 
A'a gaskiya bani da ita.
 
Rubutu, idan a ka ce rubutu, mi ake nufi a wurinki?
 
Rubutu wata hanya ce ta isar da saƙo ga al'umma. Kamar yadda za ka yi magana aji saƙonka haka ma rubutu yake, da zarar ka faɗi wata magana  ta je kai tsaye ga al'umma suka karanta to fa ka rubuta saƙo ne kuma an ɗauka har ma wasu sun yi amfani da shi wasu kuma su ƙi, koma dai mene ne rubutu dai hanya ce da za ka isar da saƙon da kake son isarwa.
Marubuci mutum ne da zai zo da wani saƙo ya amayar da shi ga wanda yake so. Marubuci ya kan saka kowace riga, idan ya ga dama ya saka ta likita, ɗansanda, soja, ɗan shaye-shaye da dai saura. Domin yaɗa abin da ke zuciyarsa, don kawo ci gaba ko gyara ga al'umma duniyar da yake ciki
Waɗansu sukan ce "Shirirta, rashin aikin yi, shi ke sa mutum ya fáɗa duniyar rubutu da marubuta, me zaki ce kan hakan?
 
Gaskiya ko kusa wannan zancen ba haka ba ne ba, shi rubutu ai wata baiwa ce da Ubangiji ke badawa ga wanda ya so, dan haka masu cewa haka ma su daina, domin kuwa rubutu wata gagarumar baiwa ce da Ubangiji ya rabawa bayinsa.
Wacce irin gudunmawa marubuci da shi kanshi rubutun ke bayarwa a cikin al'umma?
Gaskiya suna bayar da babbar gudunmawa sosai a cikin al'umma domin Marubuci zai zauna ya zaƙulo wasu matsaloli da suka addabi al'umma ya yi rubutu a kai, inda a ƙarshe ya kawo hanyar da za a bi a magance wannan matsalar, kinga kuwa ba ƙaramin gudunmawa suka bayar ba.
 
Haka ne. Madallah da marubuta. Wacce irin nasara Mai ƙosai ta samu a duniyar rubutu?
 
Gaskiya na sami nasarori sosai a duniyar Marubuta, kasancewar Rubutun Hausa na yi min wahala a baya  ma furta Hausar ita kanta sai ga shi shigata duniyar Marubuta na iya har ma ina koyawa wasu, alhamdulillah!
Ke ɗin ba bahausa ba ce?
Eh, tau ba na ce ba, ga shi dai an haife ni a Kano cikin Hausawa amma gaskiya Hausata kamar 'yar gwari haka take, wajen *ra* ba na iya furtawa abubuwa da yawa dai kam
Allah sarki.
 
Akwai nasarorin da aka samu a fannin Gasa wacce ake sanyawa tsakanin marubuta?
 
Ban taɓa shiga gasa ba sai sau ɗaya ita kuma na yi nasarar da labarina ya zo na biyar, sai kuma yanzu da na shiga wata ita kuma sakamakon bai fito. A da ba na jin sha'awar shiga gasa amma watannin baya kusan wata bakwai na ji ina da sha'awar shiga kuma in sha Allahu zan saka ɗamba.
 Wanne irin ƙalubale aka fuskanta?
Tau, ƙalubale na guda biyu ne matasalar idona, wanda shi ke hana ni rubutu. Sai kuma rashin amfani da daidaitacciyar Hausa amma yanzu in dai ta fannin Hausa ne alhamdulillah! 
 
Allah ya baki lafiya
 
ameen meen na gode sosai
 
Wasu ɓata gari sukan ari rigar marubuta su sanya, suna rubutun batsa. Wacce ta kai ta kawo zuwa yanzu an yiwa marubuta bugu ɗaya, bayan marubutan online ne ke rubutun batsa, wanne kira za kiyi da mu su cewa haka, da masu aron rigar marubuta suna ɓatawa marubuta suna?
 
Kiran da zan yi a gare su shi ne su ji tsoron Allah, su sani yin hakan ba zai amfanar da su komai ba sai dai ya kai su ga halaka, idan jindaɗinsu shi ne ɓatawa Marubuta suna to su sani Allah yana tare da Marubuta, kuma kariyarsa ce ke nashe da mu, don haka duk wanda ya yi nagari kansa, idan ka yi ka ci riba gaba ba za ka ci ba, koba komai ina son su dinga tunawa da cewar wata rana dole suna da iyali kuma za su ga abin da suka yi.
Wanne kira za ki yi da marubuta?
 
Kirana ga Marubuta shi ne su tsaya su mayar da hankali wajen yin rubutu a kan abin da zai amfani al'umma, su tuna da cewa kowane rubutu idan an tashi ranar alƙiyama za su yi bayaninsa, don haka su tsaya su yi rubutu domin gara da ci gaban al'umma yadda har tattaɓa kunnensu za su mora
 
Daga ƙarshe ki gaida marubuta uku a wannan firar.
 
Ina gaishe da Princess Aisha, Hassana Labaran Ɗan Larabawa sai kuma Abu Amrah.
 
Ma sha Allah, godiya nake
 
Muna godiya sosai da sosai
Allah ya hutar da gajiya