Bana  cikin mutanen Arewa da ke taruwa domin cewa dole ne Shugaba Bola Tinubu ya tafi---Tambuwal

Bana  cikin mutanen Arewa da ke taruwa domin cewa dole ne Shugaba Bola Tinubu ya tafi---Tambuwal

Gwamnan Jihar Sokoto na da, Aminu Tambuwal, ya ce ba ya   cikin mutanen Arewa da ke taruwa domin cewa dole ne Shugaba Bola Tinubu ya tafi.

Sai dai ya ce yana da cikakken ƙuduri, kashi 100 cikin 100, na tabbatar da cewa an sauke gwamnatin Shugaba Tinubu da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga mulki ta hanyar dimokiraɗiyya a shekarar 2027.

Da yake magana a gidan talabijin na Channels kan halin da ya shiga a hannun Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Tambuwal ya ce gwamnatin Tinubu ba ta jin daɗin ayyukansa a jam’iyyar adawa ta African Democratic Party (ADC).

Da aka tambaye shi ko zai ce shari’ar da EFCC ke yi masa ta siyasa ce, sai ya ce, “Eh.”

Da aka tambaye shi ya ambaci waɗanda ke binsa, ɗan siyasar ya ce, “Waɗanda abin ya shafa suna damuwa da ayyukana.”

Game da ko hakan na da alaƙa da burinsa na siyasa, ya ce, “Saboda ina cikakke cikin wani tsari da zai, ta hanyar dimokiraɗiyya da doka, da yardar Allah, fitar da wannan gwamnati daga mulki. Ina da cikakken ƙuduri, kashi 100 cikin 100.

“Da yardar Allah, tare da taimakon Allah da ’yan Najeriya, za mu kori wannan gwamnati daga mulki.”

Da aka tambaye shi ko gaskiya ne cewa wasu mutane a Arewa ba su ji daɗin gwamnatin Tinubu ba kuma suna kulla mata makirci, ya ce, “Gaskiya ne cewa ’yan Najeriya ba su ji daɗi ba.

“Ba na cikin wasu mutanen Arewa da ke taruwa domin cewa dole ne Tinubu ya tafi. Ina cikin ƙungiyar haɗin gwiwar ƙasa da ke neman a samu sauyin shugabanci a Aso Rock ta hanyar tsarin dimokiraɗiyya na kundin tsarin mulki a ranar 29 ga Mayu.”