ANA BARIN HALAL..: Fita Ta 47

ANA BARIN HALAL..: Fita Ta 47

ANA BARIN HALAL..: Fita Ta 47

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* 

*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin Ƙarfe

Burin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*

Idan kana/kina sha’awar:

_**Updates akan tallafin gwamnati (Grant & Loan)._

_**Hanyoyin samun kuɗi ta kasuwanci na online._

_**Sana’ar hannu da za ki iya yi daga gida._

_**Dabarun amfani da waya wajen samun kuɗi._

_To wannan group ɗin na Business/Grant/Loan naku ne! Zaku samu labarai kai tsaye + shawarwari masu amfani in sha Allah._
*Join yanzu don kada ku rasa sabbin damarmaki*
https://chat.whatsapp.com/C64wC3IDhW6FtwjSpWWDiL?mode=ac_t

*Page 47*

*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE  ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559

**********
Ina jin shi a gaggauce ya shiryah, ƙamshin danaji ya cika ɗakin mai daɗin gaske ne yasa na fahimci ya gama shiryawa, amma duk da haka ban ɗago fuskana ba, har gaba na ya ƙaraso ya tsaya,  "Eesha kinyi kyau sosai",  naji sautin muryan shi a kaina, ban ɗago ba amma nayi murmushi kaɗan ina bin yatsun ƙafan shi farare sol da kallo, hannun shi ya saka ya riƙo nawa, jin haka yasa na ɗago kaina na dube shi, aiko da sauri ya sake ni ya ɗan ja baya da sauri ya ɗan saki ƙara kaɗan, tashi nayi tsaye da sauri ina kallon yadda yake yarfe hannun shi, a hankali nace,  "wani abune ya sameka"?  aikuwa babu shiri najo yayi ƙasa da sauri yana toshe kunnen shi, bakin shi kuma yana furta,  "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un",  matsawa kisa da shi nayi da sauri nima na durƙusa ganin ya riƙe kanshi da dukkan hannayen shi yana runtse ido,  "A.G na lafiya"? Na faɗa duk jikina yana rawa,  ihuh ya saka iya ƙarfin shi yana cewa,  "ki matsa a kusa dani bana jin numfashi sosai, ki matsa ana shaƙe mun wuya na, wayyo Allah subhanallahi",  da sauri na matsa a kusa da shi jikina yana rawa,  birgima ya farayi yana jan numfashi da ƙyar, ganin haka ya saka na fice a ɗakin da sauri, parlor na naje da gudu na ɗauki wayana, rasa wa zan ƙira a wannan lokacin nayi, wani zuciyar yace na ƙira M.G, kuma nayi tunanin bai kamata ba, tou ko gidan mu zan ƙira? Nan ma nayi tunanin me zance? Kawai sai naji na fashe da kuka, zama nayi a bakin kujera hannu na riƙe da wayata, ban daɗe ba sai na ganshi ya fito daga ɗakin shi ras da shi, binshi nayi da kallo ganin ya wuce kitchen, tashi nayi nabi bayan shi, friedge ya buɗe ya ɗauki ruwa, kafa kai yayi ya shanye duka goron, nidai har lokacin kallon shi nake idona na zubar da hawaye, a jiyan zuciya ya sauƙe sannan ya fito zuwa parlon, yadda bai mun magana ba haka nima ban ce da shi uffan ba, three sitter yaje ya zauna ya ƙura mun ido,  "beauty meyasa kike chanja muryoyinki kala-kala ne? Ɗazu gaba ɗaya kin maida muryanki kaman na wata tsohuwa, daga baya kuma ki ka mayar kaman na wani namun daji, babu daɗi sauraro ga wani irin zafi kaman wuta da jikinki yayi, nikan baki sonane"?  Hawaye ne suka zubo mun a ido na sharrr, buɗe baki nayi zan bashi amsa kawai sai naga wani shadow yabi ta bayan kujera da sauri, aiko tsalle na daka na faɗa saman cinyan A.G babu shiri, hannu na saka na toshe bakina da na zabga ihun tsoro, a razane shima ya kallen yace  "lafiya Eeshaa tah"?  Waiwayawa nayi na kalli hanyan ƙofan kitchen don jin kaman an buɗe ƙofan an kuma rufe,  "A.G na, naga kaman an wuce ta jikin kujera, kuma sai naji an buɗe kitchen an rufe, ni wallahi tsoro nakeji",  rungume ni yayi yace,  "babu komai beauty, kice kike firgita kanki da kanki, ni bansan waye ta baki wannan shawara na jin tsoron ba? Gashi bayan kina tsorita kanki har nima kin fara bani tsoro wallahi, ɗazu fah....." Sai kuma yayi shiru bai ƙarasa ba,  chan yace "tashi muje ɗakina",  girgiza kaina nayi alaman a'a,  "ɗakinki zamuje"? Ɗaga mishi kai nayi alaman ehh,  aiko ɗaga ni yayi chakk ya kashe wutan parlon muka wuce chan cikin bedroom ɗina babban, kwantar dani yayi saman bed ɗin ya sumbaci goshina da hanci na da saman lips ɗina, nidai ido kawai na bishi da shi ganin ya wuce zuwa kashe wutan ɗakin, ƙatt naji ƙaran ya kashe wutan ɗakin,  sannan ya juyo ya nufo inda nake kwance, aiko uban ihuu na rabza, domin ganin ya rikiɗe ya koma mun mummunan baƙin mutumin nan da nake mafarki da shi, ga wasu labta labtan haƙura da ya buɗe baki yana mun dariya,  ihun da nake yi ne yasa ya koma da sauri ya kunna wutan ɗakin, jikina yana rawa na ɗago kai na dube shi,  "A.G kada ka kashe wutan ɗakin please, ka barshi tsoro nakeji," ido ya zuba mun na tsawon wani lokaci baice komai ba, chan kuma sai ya juya ya fice a ɗakin batare da yace mun uffan ba, kuka na fashe da shi ina maida kaina saman ƙafufuna, nidai ranan ban san yaya akayi bacci ya ɗauke ni ba.

Tun daga wannan ranan bai sake nuna zai zo inda nake ba, zamu zauna muci abinci tare, idan baƙi sunzo zamu karɓe su tare, idan dare yayi zamu zauna a parlor ɗaya muna kallo muna ɗan hira jefi -jefi, amma bao sake kusanto da kanshi kusa dani ba, a haka har ya saura kwana biyu ne tafiyan mu Abujah,  da dare muna zaune a parlon shi muna kallo naji yace,  "Eesha na gobe ki shiryah zakuje kuyi sallama da mummy da su goggo da gidan Dadda, sai kuma chan gida wurin su ummie"  Farin ciki naji sosai saboda zan fita nima, gashi jiya da hafsy tazo take ce mun wai raliya zata tafi da sabeer, amma Abba ya hana ta, gashi yanzu yaron yana ta laulayin haƙori, sai zazzaɓi da gudawa yakeyi, da ta tafi dashi wani kulawa zata iya bashi," duk dama hankalina yana kan na ga yaron ne wallahi, shine babban farin cikin zuwa na gidan kuma, don zanyiwa Abba magana yaushe zan ɗauke shi? Don Abuja muna gama hutu zan dawo bch, zai sama sai anyi hutu naje, A.G ma zuwan shi zai zama ba akai akai ba, yaron zai ɗebe mun kewa, ranan nayi bacci cike da farin ciki, kuma Aunty nice nifa wannan period ɗin har ranan bai ɗauke ba, sai dai yawan zuban shine ba sosai ba.


Washegari tun 9:00am nagama shiryawa, A.G kuma don gadara har lokacin bai ma tashi a bacci ba, sinasir nayi mai yawan gaske, don tun an idar da sallan asuba nake aikin yin shi, ga miya nah mai daɗi da kyaun gani a ido, duka gidajen da zamuje n zuba musu a cooler daban -daban,  akwai dambun kaza da aka mum, shi kuma na nemi ɗan madaidaicin bucket na zubawa Daddy ɗaya, ɗaya kuma na kakane, wato Alhaji Inuwa.

Ɗakin shi na shiga na samu ya wani ƙura A.C ya duƙunƙune yana bacci, zama nayi na yaye duvet ɗinna ƙura mishi ido, jin sanyi na ratsa shi ya sa ya ɗan buɗe lumsassun idanun shi kaɗan yana kallo na, marairaicewa nayi alaman don Allah ya tashi, jawoni yayi na faɗo kanshi, duvet ɗin yaja ya rufe mu ruf da shi, hannu na saka na sake yayewa, buɗe idon shi kaɗan yayi yana kallona,  "baby muyi bacci please", ya faɗa yana ƙara jawo duvet ɗin, ban barshi ba ya rufe ba na saka hannu na yaye duka nace.  "please mana A.G na ka tashi mu tafi, nifa na musu abun karyawa ne fah, kada su riga su karya kuma",  na faɗa ina turo mishi baki gaba, kiss ya manna mun a lips ɗinnan sannnan ya tashi zaune da ƙyar,  juyar da kaina gefe nayi saboda bana son ganin tashin shi, duk da jallabiya ce a jikin shi, amma shi yanzu ya koyi rashin kunya, a gabana sai ya cire kaya,  "yarinyar nan baki son zaman lafiya wallahi, breakfast ɗinma sai kin wahalar da kanki kinyi har da su? Hmmm amma aikin miji kam an kasa sauƙewa, sai na sarakune" Ya faɗa yana ɗan dariya kaɗan, hararan wasa nabi shi da shi har ya wuce toilet, gyara mishi ɗakin nayi tsaf na feshe shi da turare, bayan na fita a ɗakin naje shiryah duk abunda zamu tafi dasu, kunun gyaɗa na fari sol na cika flask biyu da su, ɗaya babbaɓ wanda zamuyi break agidan su A.G nah, ƙaramin kuma na ummie nane, don tana son sinasir da kunun gyaɗa.

Tayashi ɗaukan komai nayi muka kai mota, yana ta mitan an hana shi breakfast wai sai munje gida, nidai ko kula shi banyi ba na shige mota ina ta dariyan shagwaɓan shi, gidan mu yafara zuwa ya tsaya a Gate, ɗaure fuska yayi sosai bai kalle ni ba, ƙiran hafsy yayi a waya ta fito, coolern na ummie da flask ɗin kunu ya bata, yace ta gaishe da ummie sai mun shigo anjima, gwaliyo take ta mun har ta koma gida, kallon fuskar shi daya murtuƙe kawai nakeyi, nasan don kada nace zan sauƙa ne yasa yayi haka, daga nan unguwar winti mukaje  gidan kakan shi, nan ma a waje ya barni ya ɗauki cooler da ɗan ƙaramin bucket ɗin dambun ya shige dashi, bai wani daɗe ba ya fito ya miƙa na gidan goggo, sai da muka ɗauki hanyar gidan su tukun ya juyo yana kallona fuska a sake yace,  "ƴan mata na mai tsoron aure yayah kike"? Hararan shi nayi cikin wasa na juyar da kaina, murmushi yayi ya saka ɗayan hannun shi ya matsa chinya na yace,  "Eesha wai yaushe period ɗin nan naki zai ɗauke ne kam? Nifa na matsu fah,  haba M.G sai wani kallon banza yake mun kullum wanda na rasa dalili".
Dariya nayi ina ture hannun shi da yake wani matsa mun cinya kaman mai shirin matsan gyaɗa,  "ni ae ban san yayah zanyi bane"? Na faɗa ina sunkuyar da kaina, bai juyo ya kalle ni ba yace,  "ki daure ki cire tsoro na a ranki zai ɗauke",  shiru nayi bance uffan ba, gannin haka ya juyo ya ɗan kalle ni kaɗan, dai dai maigadi yana buɗe mishi gate da yayi horn a lokacin, muna shiga muka hango motar M.G a parke, murmushi A.G yayi yace,  "wayaga bita zoi-zoi M.G har an hankaɗo shi ya iso",  ya faɗa yana wani munfukin murmishi, wanda nayi imani iyakan ta nan cikin mota ne, muna fita zai koma kaman ba shi ba, muna parking ya juyo ya kalle ni,  "wallahi kada naji kina ziban zance a gaban ƙananun yaran nan, don bana son raini, idan sun raina mun mata ni suka raina kinji ko"? Ɗaga mishi kai nayi alaman naji,  ganin haka ya ɗan sunkuyo ya sumbaci lips ɗina, murmushi ya mun nima na mayar mishi, sannan muka buɗe motan muka fita tare, taimaka mishi nayi muka ɗauki kayan da muka zo da su.

Muna shiga parlon na hango M.G zaune Shi da Daddy, T.V kunne  yana aiki, su kuma Suna hira, lokacin kuma mummy ta fito daga hanyar kitchen heedaya na biyota a baya hannun ta ɗauke da filet da soyayyen ƙwai sai cup da tea a ciki,  direct dinning muka wuce muka ajiye kayan da yake hannun mu, ɗan ihu kaɗan heedayah tayi tana mun oyoyoyo, hararanta da A.G yayi ne taɗan nutsu, amma idon ta nakaina tana murmushi, nima murmushin nayi idona yana kanta,  "har kun iso kenan"? Na tambaye ta bayan na ajiye abunda yake hannu na na juyo hannu na riƙe da handbag ɗina,  "ai ina ga da ƙyar idan ba a ƙofan gidan nan 8:00am ta musu ba, gashi ni tunda tazo bata barni na huta ba",  mummy ta faɗa tana dungure kan heedayah,  Murmushi nakeyi na ƙarasa har parlon inda mummy suka ƙarasa da A.G suka zauna, har ƙasa na je na tsuguna na gayar da Daddy, amsawa yayi cike da jin daɗi, haka itama mummy na gaisheta tana amsa cike da jin daɗi, M.G na gayar, murmushi ɗauke a fuskan shi ya amsa da, "yauwa matar babban yayah, kun samu iso ko"?  Nidai murmushi nayi bance uffan ba, hararan shi A.G yayi ya kawar da kai, bayan heedaya ta gaishe da A.G ne ta mun alaman mu wuce ɗakinta, ban wani ja ba nabi bayanta muka wuce,  "Aunty naje na soya miki egg ɗin ne ko zamu ci wannan na zubo miki tea"?  Murmushi nayi nace,  "ga abun breakfast na taho mana da shi, kada ki wani wahalar da kanko, ci kawai ke kaɗai",  dariya tayi tace,  "aiko naga kuloli kawai ban isa nayi wani rawan kai akai bane tunda tare kuka zo da yayah, amma ae dana biɗe na fara ci, yanzu sai sun gama hirarrakin su tukun ace mu fito" ta faɗa tana hararan tea ɗin hannun ta, nidai murmushi nayi bance mata uffan ba, aiko baifi wasu mintuna ba mummy ta ƙwala mana ƙira, da sauri muka fita zuwa parlon.

A dinning muka same su dukkansu suna zaune, fuskanta cike da farin ciki ga murmushi a kai tace, doug ashe hidima sosai kika mana haka? Gaskiya abu yayi kyau Daddyn kuma sai yabawa yake tayi", ta faɗa tana zubawa daddy a filet, shima Daddy godiya yayi har yasa naji kunya a lokacin, kallon mu tayo bayan ta zubawa mijinta da kanta yadda zai musu, ta cika musu cups da kunun gyaɗan tace,  "tou kowa tazo tayi saving kanta da mijinta, kuna na kuma kada a zuba dayawa, a saka dai-dai a bar wa mijina sauran,"  ta faɗa kowa yana mata dariya, da sauri heedayah ta matso zata zuba, hararanta A.G yayi yace,  "ke matsa a wurin don Allah, ki bari wanda ta hanakanta bacci tayi ta fara zubawa, ke ae haka kika bar kanki da mijinki don lalaci da shirme kika taho", aiko baya taja ta tsaya, daga Daddy har Mummy dariya sukeyi, shi ko M.G hararan A.G yakeyi baice mishi komai ba, mayar da kallon shi yayi kan matar shi yace,  "dawo nan kafin ya kai miki naushi a kyakkyawan fuskanki, su gama zubawa mu ko sauran nasu ne bamu da matsala zamu ci," ya faɗa ya na maida ita gefen shi ta tsaya, ni dai cike da kunya na zubawa A.G na, gaban shi na ja filet ɗin da cup na ajiye,  sannan na zuba ƙwaya biyi anawa filet ɗin, ban zuba kunu ba nace,  " heedayah ki haɗa mun tea mana"  mummy ne rayi charaf tace,  "a'a doug bazaki sha kunun bane? Ko kinfi son tea ɗinne"? Ina murmushi na amsa mata da ehh, dama nayi saboda sune kunun, ni nabar nawa a gida ae, tea ɗin heedayah taje ta haɗo mun, sannan tazo taa zubawa M.G na shi a filet ɗin, kunu ta zuba mishi ta miƙa misho, ta ɗauko cup zata zuba A.G ya dakatar da ita,  "kema ki zuba tea ɗin yadda kika ga ita ma tayi karan barwa Daddy, idan kunun kike so idan kin kuma gidanki ki dama",   dariya sosai mummy da daddy sukayi, inda Daddy yace "godiya nake ranka ya daɗe, ita bata kawo ba zata shanye mun kununa mai daɗi" ya faɗa yana kurɓan kunun,  mummy kuma cewa tayi, "ni banga ta inda wani abu zai shiga cikinta bama idan ba fitina ba, shigowan ku fa ta gama soya egg ta haɗa da tea, shiyasa daga ita har mijinta suke labta uban ƙiba, tsabar cinsu yayi yawa, sun bar mun kai da matar ka baku ƙara ko taki ɗaya ba, sai ma ramewa da kuka sakeyi",  kunyar maganan mummy naji har na ɗaga kai na kalle shi, shima kallo na yayi ya mun alaman ae duk nine na jawo.
 "Daɗin abun ma ae an bawa mijinta, kuma bazai shanye duka ba zai bar mata ko Giwata? Kuma muna zuwa gida zan zo na karɓe na matar ka data ajiye a raba musu",  ya faɗa yana duban A.G yana dariya, harara A.G ya zabga mishi sannan yace "ke jata kuje ɗakinki zata fi sakewa ta ci sosai, saura kuma ki cinye naki kici nata", ya faɗa yana ƙara mun sinasir biyu akan wanda na zuba, ita dai heedayah ta tura baki gaba, parlon kuma duk dariyanta sukeyi, haka muka wice ɗakinta wanda hakan kuma wallahi ya fi mun daɗi.

Muna shiga kuwa tace,  "kaii Allah ya baki fitinannen miji wallahi Aunty, kuma akwai sauran kunun ne a gida kika bari"? Nidai murmushi nayi na zauna akan lazy chair da yake garkame a ɗakin nata ƙwaya ɗaya, "akwai amma baifi cup 2 ba, wa mijina na ajiye dama ba wa kaima ba, saidai ku raba ke da shi idan mun koma",  na faɗa ina fara kai sinasir ɗina baki, "chaɓɓ sai dai kawai na lallaɓa daddy anjuma idan babu kowa ya sanmun, amma cup biyu kam bazai bani ba, kinsan yadda yake shan kunu kuwa shi da Daddy? Ae yafi son kuni ma akan tea, Giwa ne kawai yake son tea, amma mijinki kam dama kunu ya sameki, nima ina so, idan na dama baya kyau ne kawai yasa banayi," ta faɗa tana zama a bakin gadon.

Bayan su daddy sun gama sun kuma parlor ne na fita na samu mummy zata tattare, hanata nayi na kwashe nakai kitchen, ina jin A.G ya ƙwalawa heedaya ƙira ta fito da sauri, nuna mata hanyar kitchen yayi ya juya, shigowa tayi muka wanke komai muka gyara, tambayanta nayi mai zamu ɗaura na rana? Ya mutsa fuska tayi tace,  "don Allah Aunty fito mu tafi, akwai fa mai ƴiwa mummy girki, breakfast ne kawai ta keyi da kanta, don Allah fito bacci nakeji, yanzu ina fita mijinki zai koroni", 
Dariya nayi nace,  "gaskiya yai mu zamiyi abinci, nemi wuri kawai ki zauna, idan zaki iya ki fakaici idon shi ki wuce, haka ko akayi ficewa tayi ta gudu, dariya ma ta bani sosai.

Friedge na buɗe na ɗauki mama na wanke na ɗaura akan gas, sannan naga akwai markaɗaɗɗen kayan miya shima na fito da shi, ina haka sai ga mummy ta shigo,  "doug kaii jeki huta akwai wacce zata zo ta ɗaura" ta faɗa tana ƙarasa shigowa,  "mummy yai kam ta huta, babu komai zan yiwa Daddy abinci da hannu na yasaka albarka", na faɗa ina ajiye kayan miyan,  "doug wanda kika kawo mana for breakfast ma ae ya saka albarka, Allah ya muku albarka gaba ɗaya, Allah ya zaunar daku lafiya a gidajenku,"  haka dai na ribace ta tabari na ɗaura, muna zaune ta ɗauko shuwaka ta gyara, ina ganin haka nagane tuwo takeso ayi kenan, haka na zage na tuƙa tuwon shinkafa mai kyaun gaske, muna hira da mummy da taja kujera ta zauna, duk abinda na nema sai ta nuna mun, haka na haɗa miya ne wanda yaki cyryfish da egusi da stockfish ga nama sosai, muna ciki A.G ya shigo, "ina wannan malalaciyar ita kuma take"?  Mummy na murmushi tace,  "don Allah amata haƙuri ta kwanta bacci ne" 
"mummy ita ba mace bace  da ku zaku fito kuna aiki ita kuma taje ta kwanta don son jiki? "  
Mummy tana murmushi tace,  "kasan kowa da yadda abu yake zuwa mishi, ita na lura ciki ta samu na gaggawa, kuma yazo mata da bacci da yawan ci, wata macen ranan da aka kaita ranan take samun ciki idan an dace, tou inaga ƴar'uwaka haka nake tunani, saboda haka kayi haƙuri kaima naku da irin na shi salon zaizo" kunya naji ya kamani, don kuwa yace mun ita fah Mummy bata jin kunyar watso zance, saboda haka idan kinje kiyi haƙuri ki saba da haka, sunkuyar da kaina nayo, amma kawai sai naji A.G da wani zance,  "mummy ita wannan ae ban san meye matsalanta ba, tunda aka kaita fah har yau period ɗinta bai tsaya ba, ke da yake tsohuwar ma'aikaciyar jinya ce may be zaki san meye matsalan"?

Shiru nayi tsabar kunya naji kaman zan nitse a ƙasa, murmushi mummy tayi tace "shikenan son babu komai, insha Allahu zamu yi magana da ita, zanje koma menene,"  "yauwa mummy idan kuma tsoro ne ta saka a ranta please ki hanata ni wallahi......" sai kuma yayi shiru yana kallon mummy yakasa cewa komai.
Dariya tayi tace,  "babu komai son zamuyi magana da ita, bari ta gama abincin mu shiga ciki, idan akwai matsala ma zan sani idan babu ma duk zan sani, ka gajji kuma tou kayi haƙuri, kasan mata da matsala iri-iri",  murmushi yayi ya juya ya fice, nidai ji nayi bazan ma iya juyowa na kalli mummy ba wallahi, kai amma A.G bai san meye kunya ba naga alaman shi wallahi, har wa mummy yake iya irin wannan bayanin? Gashi yana magana kaman zai mata kukan nan na shi na jaraba, naga alaman shima idan a kusa da ita yake shagwaɓaɓɓene.


*AUNTY NICE*