Saudiyya ta amincewa Ronaldo ya yi zaman dadiro da sahibar sa Georgina

Saudiyya ta amincewa Ronaldo ya yi zaman dadiro da sahibar sa Georgina

Rahotanni daga kasar Saudiyya na nuni da cewa Cristiano Ronaldo da sahibar sa, Georgina Rodriguez za su sami takardar izinin zama tare, duk kuwa da dokar da ƙasar ta yi mai tsauri a kan zaman dadiro.

Dan wasan mai shekaru 37 ya koma Al-Nassr ta Saudiyya kan kwantiragin shekara biyu da rabi ta kimanin fam miliyan 173 a kakar wasa bayan kwantiraginsa da Manchester United ta rushe.

Sai dai kuma zaman Ronaldo tare da Georgina zai kasance karya dokar auratayya a Saudiyya.

A cewar jairdar wasanni ta Sport, Ronaldo mai ƴaƴa biyar, da kuma Georgina, wa ce ta haifa masa ƴaƴa biyu, za su samu izinin zaman ne duba da cewa ya na ɗaya daga cikin ƴan wasan da suka fi kasuwa a duniya.

Rahoton ya ci gaba da ambato wasu lauyoyin Saudiyya biyu, wadanda ke hasashen hukumomi ba za su tsoma baki a kan lamarin ba.

Wani daga cikin lauyoyin ya ce: “Ko da yake har yanzu dokokin sun haramta zaman dadiro a Saudiyya, amma hukumomi sun fara kau da kai kuma ba za su hukunta kowa ba.

"Hakika, ana amfani da waɗannan dokokin ne lokacin da aka samu matsala ko kuma wani laifi."

Lauya na biyu ya kara da cewa: "Kawo yanzu, hukumomin Saudiyya ba su tsoma baki a cikin wannan al'amari ba (wanda ya shafi yan kasashen waje), amma doka ta ci gaba da haramta zaman dadiro a ƙasar," in ji shi.