Kidayar 2023: NPC ta kaddamar da shirin daukar ma'aikata 'yan asalin jihar Yobe

Kidayar 2023: NPC ta kaddamar da shirin daukar ma'aikata 'yan asalin jihar Yobe

Kidayar 2023: NPC ta kaddamar da shirin daukar ma'aikata yan asalin jihar Yobe

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Hukumar Kidayar Jama'a ta Kasa (NPC) reshen jihar Yobe ta kaddamar da shafin sadarwa ta zamani domin daukar sabbin ma'aikatan da za ta yi amfani dasu a ayyukan kidayar jama'a na shekarar 2023 a ranar Laraba.

Da yake zantawa da manema labaru a ofishin hukumar, Kamishinan Hukumar Kidaya ta Tarayya (NPC) a jihar Yobe, Alhaji Mai Aliyu Muhammad, ya ce kaddamar da tashar daukar ma’aikata ta yanar gizo a matakin jihar, domin daukar ma’aikatan ta a cikin sauki wanda kuma kowa da kowa zai iya yin rijistar tare da samun gurabun aikin ba tare da la'akari da bambancin yare ko jinsi ba- matikar sun cika ka'ida da cancanta. 

Aliyu Muhammad ya yi nuni da cewa, hukumar ta aiwatar da wannan matakin ne domin samun sahihin aikin kidayar jama’a, wanda yake da bukatar daukar kwararru kuma hazikan ma'aikata.

Ya kara da bayyana cewa hukumar ta bullo da wannan tsarin ne ta hanyar amfani da kafar sadarwa ta zamani wajen tallata bukatar ma’aikatan da suka dace wadanda zasu kula da cibiyoyin horaswa, jami’an sa ido da tantancewa, manajojin tace ingancin bayanai, tare da mataimakan su hadi da masu sa ido gami da kididdigar jama'a a fadin jihar. 

Alhaji Mai Aliyu ya kara da cewa, baya ga tawagar da ake da su a matakin jihar, ma'aikatan da suke bukata zasu hada da na kananan hukumomi, wadanda za su kula da ayyukan hukumar a matakin Kananan Hukumomi a jihar.

"A iya saninmu, samun kwararru da hazikan ma'aikatan da za su gudanar da ayyukan kidayar ya na da muhimmanci kuma ta wannan ne za a samu nasarar aikin. Saboda haka, dole mu nemi ma'aikata masu nagarta wadanda suka san makamar aiki game da abubuwan da suka shafi kidayar, sarrafa na'urorar kwamfuta wajen samun nasarar kidayar 2023." In ji shi.

Ya kuma tabbatar wa mazauna jihar Yobe cewa hukumar za ta yi aiki tukuru don kamanta adalci wajen zakulo yan asalin jihar wadanda suka cancanta, ba tare da nuna son kai ko bambanci ba. 

Haka kuma, Kwamishinan hukumar ya ce za su yi aiki kafada da kafada da jami'an tsaro wajen ganin aikin ya gudana cikin nasara a dukan fadin jihar. Haka kuma ya bukaci cikakken hadin kan al'ummar jihar Yobe domin samun nasarar aikin kidayar. Ya bukaci al'umma su bai wa ma'aikatan su gudummawa wajen aikin kidayar ta yadda za a tabbatar da cewa an kidaya mutanen yadda ya kamata.