Zan yi takarar Gwamnan Sakkwato a 2023---- Musa S/Adar

Zan yi takarar Gwamnan Sakkwato a 2023---- Musa S/Adar

Honarabul Musa Sarkin Adar dan majalisar tarayya dake wakiltar kananan hukumomin Gada da Goronyo a jihar Sakkwato a tattaunawarsa da manema labarai ya tabo muhimman abubuwa da suka shafi jam’iyarsu ta APC da batun yajin aikin malaman jami'a da batun takarar gwamna da sauran bayanai, ga yanda hirar ta kasance.

Mi z aka ce kan jam’iyar APC a jihar Sakkwato?

APC a jihar Sakkwato daya ce a hade muke a karkashin jagorancin Sanata Aliyu Magatakardan Wamakko, a sanina ba mu da wata baraka ko ja-in ja dukanmu masu ruwa da tsaki muna yanke shawara kan lamari a tare, in ka ga mutum daya yaki zuwa kan wani uzurin kansa abin da ya shafe shi ne, ko kuma wani uzuri ne nadaban, in mutum yana takara da wani don ya kasa fitowa ba wani abu ba ne, APC a Sakkwato ba ta da baraka daya ce a hade da karfinta muna shirin tun karar zaben 2023 gaba daya ba da wani tsoro ba, kan haka muka yarda da ra’ayin tsayar da ‘yan takara ta hanyar sasantawa, abin da ake nufi a bar wadanda ke sama su ci gaba matukar ba a samu mutum da wani laifin cin amanar jam’iya ko sabawa dokar kasa ba, sai ko in mutum ya nuna bai shawar cigaba da mukamin da yake sama sai a sauya shi, a duk duniya an aminta da siyasar sasantawa ba wani abu ba ne sabo ko sabawa dimuradiyya ba, mun gamsu da tafiyar jagoranmu yana mutunta mu muna girmama shi.

A majalisa ta tara ‘yan majalisar tarayya 11 da suka fito daga Sakkwato sun samar da kudiri 3 ne kacal mi kake ganin ya kawo hakan

Bari na sanar da kai gaskiya mutane ba su fahimci aikin dan majalisa ba ne, ba dole ne mutum ya samar da kudirin doka shi kadai ba, in aka kawo kudiri sai an yi muhawara kansa duk wanda ya ba da gudunmuwarsa a kudirin ta goyon baya ko akasin haka yana cikin wadanda suka samar da kudirin. ‘Yan majalisa a Nijeriya yanzu ne suke gagijewa a cikin shekara 20 na wannan siyasa bangaren bai gama samun kayan aiki ba da zai ba da abin da ‘yan majalisa ke bukata ba. Rashhin samar da kudiri na ‘yan majalisa daga kasawar majalisar ne da ba ta ba su cikakkun kayan aikin da suke bukata.

Harkar yajin aikin malaman jami’a

Lokaci bai yi ba da za a rika samar da jami’a bayan an kasa cika bukatar wadanda ake da su ba, kamata ya yi a samar da kayan karatu yafi a rika samar da jami’o’in suna kawai, wadanda muke da su suna bukatar gyaran tsarinsu a misali jami’ar Danfodiyo tana karantar da darasi kan harshen Hausa ko Tarihi ko kimiyar siyasa haka za ka samu a jami’ar Kano da Zariya, bai kamata haka ba, da za a fadada karatun ya zama duk darussan da ake koyarwa a wata jami’a ba za ka samu a wata ba, in kana son karatun Tarihi a misali za ka tafi jami’a kaza, ta haka za a iya samun ilmin da ake bukata ba tare da bata dimbin arzikin da kasa  ke da shi ba, kudin da za a iya baiwa jami’a daya ta inganta sai ka samu an rabe su ga jami’o’in kasa  ba biyan bukata, yakamata mu dubi zahirin lamari don yiwa kanmu adalci ba kawai fadin gwamnati ta kasa ba musamman kungiyar malaman jami’a suna ta yajin aiki sama da shekara 40 amma sun kasa zama su bibiyi wannan matsayar don ganin abin da aka samu don canja salo, kawai suna ta son a samar da jami’o’i don su je su rika shugabanci da koyarwa, a ina Nijeriya za ta je da jami’a sama da 60, ina za a samu kudin tafiyar da su amma suna goyon bayan samar da su lamari ne da yakamata a duba.

Aiyukkan mazabarsa

Abin da nafi baiwa muhimmanci ilmi na gyara makarantun furamare a yankina, nakan bayar da tallafin karatu ga dalibban da suka fito a kananan hukumomin Gada da Goronyo, na samarwa makarantun Islamiyoyinmu wutar lantarki mai aiki da hasken rana da a duk shekara nakan samar da rijiyoyin murtsatse don ragewa mutanen yankina matsalar ruwan sha, na gyara hanyar mota da mutane na, ke shan wahalarta  a Gada, da sauran aiyukkan da mutanen mazabata za su gaya maku irin hobbasar da nake yi gwargwadon hali a fanin noma da tsaro da samarwa matasa aikin yi. A gefen ilmi na dauki nauyin karatun matasa da ba zai gaza mutum 500, ban gamsu da sai na yayata abin da na yi kan ilmi ba duk yaron da ya turomin takardar samun gurbin karatu zan yi wani abu kansa a kalla na bashi rabin kudin makaranta.

 

Maganar dattawan Nijeriya kan siyasa

Dattawan Nijeriya ba su da wata rawa da suke takawa a harkar zabe, sun  tasiri a can baya amma ban da yanzu su dai su rike girmansu na ba da shawara, matasa sun karbe siyasa mafi rinjayen matasan ba za su saurari kungiyoyin dattawan ba, duk in da ka ga taron siyasa kashi 95 matasa ne kuma ba ruwansu da kungiyoyin dattawan nan ba su ma san suna yi ba, gara ma su rika Magana kan hadin kan kasa su fita batun siyasa domin ba su santa ba, su maida hankali kan zaman lafiyar kasa.

Ana fada kana cikin wadanda za su yi takarar Gwamnan Sakkwato a 2023?

Wannan ne karon farko dana ji maganar gare ka, amma nakan ga wasu in suna maganar wadanda ake hasashen za su yi takarar gwamnan Sakkwato a 2023  sai naga sunana a jerin mutanen  amma ni ban yi da kowa zan yi takara ba, muna jiran lokaci ne in ya zo mutane suka ga ina da kwarewa da cancantar in yi takarar suka neme ni  zan karba kiransu.

   

 Maganar tsaro a yankinka da kake wakilta

Da muka fahimci shugabannin tsaron sun gaza ina cikin wadanda suka yi ta kira ga shugaban kasa ya canja sugabannin tsaron kasa, akwai sanda mutanen kauyen Gada da ba su iya kwana da idonsu amma a halin da ake ciki irin koarin da mutanen karamar hukumar Gada muka yi lamarin ya ragu sosai, mu wakillan jama'ar Sakkwato a majalisar tarayya muna haduwa mu tattauna matsalar tsaro tare da dukkan jami'an tsaron kasa.