WATA UNGUWA: Fita Ta 40

WATA UNGUWA: Fita Ta 40

 

PAGE 40

SECOND TO THE LAST PAGE

 

BABI NA ARBA'IN

 

"Bangane ba, ya aka yi kasan sunanta baby? Ƙanwata ce fa, me kake cewa ta shirya? A'ina ma ka taɓa ganin wannan fuskar?"

Maisha ta jero masa rikitattun tambayoyi a cikin rikitacciyar murya yayin da rikitattun tambayoyin suka ƙara rikita rikitaccen saurayin.

Ya zube a kan kujerar da yake tsaye kusa da ita yana dafe kansa da hannu bibbiyu.

Ƙwaƙwalwarsa ta shiga nazari da yin wasu bincike yayin da wani sashe na zuciyarsa ya auno masa tambayoyi.

'Ko dai gizo take yi mini? Idan gizo ne ya aka yi Mardee ma ta ganta har take tuhuma? Me ya sa al'amarin da na daɗe da manta shi yake son dawowa ya hargitsa mini lissafi? Me ya sa Mahee ta sake shigowa rayuwata a daidai lokacin da na yi haramar watsar da duk wasu miyagun ayyuka nawa don fuskantar sabuwar rayuwa?'

 

Ganin ya yi nisa da alama yana linƙaya a kogin nazari ne ya saka Maisha ta miƙe tare da cire zumbulelen hijabin da ke jikinta ta jefar a kan kujera. A take fitinannun kayan da ke jikinta suka bayyana.

A dai-dai lokacin ne kuma Jafsee ya ɗago da kansa da nufin cewa wani abu. Karaf idanunsa suka sauka a kan Mardeensa da a lokaci ɗaya ta rikiɗe ta canza masa daga mai tarbiyya zuwa irin matan da yake rayuwa a cikinsu.

Ya zabura ya miƙe a ruɗe a mamakince

"Mardiyya..." Ya ambata da tsinkakken sauti.

Ganin sun tafa ita da Mahee suna dariya ya fahimci tabbas da wata a ƙasa, wannan ƙulalliyar makirci ce da aka ƙulla ta musamman saboda shi.

Har bakinsa na kakkarwa wurin faɗar

"Wai duk meye haka? Wane zunubin na aikata miki haka da kika shirya wannan mummunar ɗaukar fansa? Da ma ke da Mardiyyata 'yan'uwa ne?'

Duk yana yin waɗannan tambayoyin ne yayin da idonsa ke kafe a kan Maheerah.

 

Sai a lokacin ta zauna a kan kujerun falon tana wani irin ƙayataccen murmushi ganin ya fahimci ɗaukar fansar ta ƙarara.

Ta ɗora kafa ɗaya akan ɗaya tana jijjigawa.

"Da kyau Ja'afar ashe baka manta sunana ba? Na yi farin ciki da ka samu damar gane ni don ka fahimci wacece ni a yanzu, kuma ka dandani dacin fansa ta. Da ma idan maye ya ci ya manta uwar ɗa ba za ta taɓa mantawa ba.

Ba zan iya sanar da kai komai ba sai a gaban waɗancan tsofaffin naka, idan ka shirya saurarena sai na saka a kira su."

 

Cikin hanzari ya sunkuyo ya zube a gaban ƙafafunta yana faɗar "Na haɗa ki da girman Allah Mahee kada ki ƙarasa yaye bargon kamalar da nake lulluɓe da shi.

Iya abin da yayanki ya yi mini ma ya ishe ni nadama, ba irin uƙubar da ban ci ba a hannun jami'an tsaron saboda ya zarge ni ne da sace ki, da ƙyar na sha bayan an bincika an gano ba ni da laifi ko ɗaya. A lokacin ne kuma Abbana yasan halin yaudarar 'yanmata da nake yi, da ƙyar ya yafe mini domin ko a duniyar mafarkinsa bai taɓa tsammanin haka daga gare ni ba.

Yanzu idan kika yi mini haka kwaɓata za ta yi ruwa, zai iya sallama ni ga duniya bayan ya saurari bayananki, ki yafe mini..."

 

"Fatana kenan Jafsee, ina fatan iyayenka su sallama ka kamar yadda ka janyo nawa iyayen suka sallama ni kuma suka cire ni daga cikin zuri'arsu."

 

A daidai lokacin ne kuma Sorfina ta shigo falon a hanzarce gudun kada a yi ba ita, gara dai ita ma ta wasa kunnenta da labarin da ta daɗe tana tsumayen jinsa, kuma aka daɗe ana ɓoye mata shi wato labarin Mahee luv.

 

Mahee ta ci gaba da cewa "A wancan lokacin da na je wurinka ina kuka ina yi maka magiyar ka taimaka ka aure ni mu rayu a tare don cika burikanmu shin ka saurare ni ne? Kamar haka ne a yau da damata ta zo ba zan saurari uzurinka ba."

Tana kaiwa nan a zancenta ta ɗaga waya ta kira Tukur tana faɗar "Ka shigo da waɗannan bakin zuwa babban falona."

 

'Falonta? Tana nufin gidan nata ne ko Miye? Yaushe ta yi aure waye mijinta? ko wanda ya ɗauko mu daga tasha ne mijin nata?'

Tambayoyin da suka ziyarci zuciyar Ja'afar kenan.

Jim kaɗan sai ga su Bala sun shigo tare da ɓakin.

Suka zauna Mahee ta gaida su cike da ladabi sannan ta ce "Ku gafarce ni Abba, abin da kuka zo nema ba zai samu ba. Ina nufin aure ba zai yiwu tsakanin Mardiyya da Ja'afar ba."

 

A tare Abba da ƙaninsa suka ƙwalalo ido cike da mamaki, kowannensu yana mamakin ƙarfin hali irin na wannan matashiyar budurwar da a shekaru ba za ta kai ga wacce suka zo neman aurenta ba.

'Shin ita ce me bada aure? A maimakon iyayen yarinyar su yi musu wannan bayanin me ya saka wannan yarinyar ce take bayani. Da alama ma hukuncin ita ce ta yanke kuma ba wanda ya ce mata kanzil, duk me wannan ke nufi? Yana da kyau su san dalilinta.'

 

Wannan dalilin ya saka Abba ya buɗi baki ya ce "Subhanallah! Duk na ji batunki yarinya amma nasan kamar yadda banza bata kai Zomo kasuwa kamar haka ke ma ba a banza kika yi hukuncin nan ba."

 

"Tabbas kuwa baba da ma wannan soyayyar gangan ce kuma ni na haɗa ta, saboda na fahimtar da yaronku cewa duk abinda mutum ya shuka shi zai girba, kuma duk nisan dare gari zai waye, sharri kuwa ɗan aike ne kana aika shi zai dawo maka..."

 

Nan ta shiga ba su labari tun daga ranar haɗuwarta ta farko da Ja'afar har zuwa tarayyar soyayyar su da muguwar yaudarar da ya yi mata har zuwa shirin ɗaukar fansar ta da abubuwan da suka faru a yau.

Sannan ta ƙara da cewa "Yanzu fansata ta cika, na cika burina na farko da ya cillo ni harkar bariki saura ɗayan burin kuma. Washe gari sai ku shirya ku koma gida, kai kuma Ja'afar fatan ka ɗanɗani azabar da ake ji yayin rabuwa da masoyin da aka shaƙu da shi."

Daga haka ta miƙe za ta koma ciki, su Maisha suka rufa mata baya.

 

Abba da ƙaninsa tsit suka yi sun kasa furta koda kalma ɗaya ne, da alama sun shiga jimami.

Har sun kai ƙofa suka biyo sautin Muryar Ja'afar na doso su cikin kuka yana faɗar

"Ki yi haƙuri Mahee ki yafe mini, don girman Allah kada ki raba ni da masoyiyata, na yi mugun sabo da soyayyar ta, zan iya rasa raina a silar rabuwarmu..."

Dai-dai lokacin ya iso gabansu ya durƙusa ya ci gaba da cewa "Ba zan iya rayuwa ba Mardee ba, ko da kuwa na rayu to rayuwata ba za ta yi armashi ba, za ta kasance kamar shayin da ba sukari a cikinsa. Na yi alƙawarin sauya ɗabi'una bayan mallakarta. Pls Mardee ki saka baki ta haƙura, ki faɗa mata kina ƙaunata..."

Haka ya yi ta zuba cikin sautin kuka.

Maisha ta yi maƙeta cin murmushi ta ce "Sunana Maisha ba Mardee ba, ni bana sonka kuma ba aure a gabana. Mardiyyarka ce ke ƙaunarka kuma a yau mun sheƙe ta kamar yadda muka busa mata rai. Da ma ni nayi ne saboda kuɗi."

Daga haka suka sheƙe da dariya su duka ukun suka shige ciki.

Nan suka bar Ja'afar da sandararrun iyayensa. Ja'afar sai kuka yake da nadamar rayuwa washe gari tun da sassafe su Bala suka ɗebe su a mota don raka su tasha ba tare da Ja'afar ya samu damar sake daura idonsa akan Mahee da Maisha ba.

Sai dai me a maimakon su ɗebi hanya samɓal zuwa gwadaben da zai sada su da tashar sai suka yanki hanyar jeji.

Ja'afar ba ya iya fahimtar komai saboda damuwa da ta yi wa zuciyarsa ƙawanya ko banza ma shi baƙo ne a garin.

 

Suna cikin tafiya kawai sai suka hango 'yandaba a gabansu, cike da kiɗima Bala ya taka birki yana faɗar "innalillahi wa Inna ilaihir raji'un!"

Kan ka ce me 'yan daban nan sun rutsa motarsu suka mammari su Bala sa'annan suka lakaɗawa Ja'afar da iyayensa ɗan banzan duka. Ba ma kamar Ja'afar sai da suka haɗa masa jini da majina kamar ba za su bar shi da rai ba. Sannan suka ɗebe su zuwa bakin gefen babbar hanya suka yasar.

Su kuwa su Tukur tunda aka mammare su suka dafe ƙeya suka ranta ana kare cike da tashin hankali.

Su ne kuma suka koma suka kaiwa su Mahee labarin abin da ke faruwa.

 

**** ****

Al'amarin Irfan kuwa yana isa Office ya je wurin manager ya bada wasiƙarsa ta neman Hutu.

Washe gari aka masa izini tare da bashi isasshen Hutu har na wata ɗaya cif.

Cike da wani irin yanayi da baka isa ka fassara shi kai tsaye ba ya dawo gida ya shiga tattara komatsantsa. Sai da ya gama shirin shi tsaf kafin ya sanar da Alhajinsa ya ɗauki Hutu zai je Balgori wurin abokinsa. Ya samo wani uzurin ya faɗa masa.

Don yana da tabbacin matuƙar ya fede masa gaskiyar labarin ba zai bar shi ya je ba. Shi kuwa ya ɗauki aniyar rusa duk wata katanga da za ta yi masa shamaki da ƙudurinsa.

A daren wannan ranar ya je gidan su Mahee.

A ƙofar gida ya sami Sadiƙu suka gaisa sannan ya sanar da shi ƙudurinsa, ya kuma nemi da ya kira masa baba ya nemi sa albarkarsa da addu'ar sa koda za a da ce.

Sadiƙu ya yi matuƙar farin cikin jin cewa Irfan ya samu labarin inda za a samo gudan jininsa, yar uwa ɗaya riko da yake da ita a rayuwa.

Don haka cike da zaƙuwa ya shiga cikin gidan ya sanar da baba zuwan Irfan har ma da ƙudirin da ya kawo shi.

Bayan wani ɗan lokaci sai ga shi ya fito cike da fara'a ya ce "Baba yana maraba da kai, shige mu je cikin gida, a yi komai gaban Umma."

Bayan ya shiga ciki ya zauna akan tabarmar da Baba yake zaune suka gaida sosai sa'annan ya sanar musu da ƙudurinsa na fita neman yar tasu a inda ya samu labarin ta. Ya ƙara da cewa "Sanyawar albarkaku da addu'arku nake nema ko na yi katari da samunta a can. Sannan Baba dole ne sai ka yafe wa Maheerah sa'annan za a samu sauƙi cikin al'amarin nan."

A dame baban ya ce "Yaro ni tuni ma na yafe mata, na gano kuskurena. Da ma shi ice tun yana ɗanye ake tanƙwara shi idan ya riga ya bushe ba ya tanƙwaruwa. Ka ganni nan kullum addu'ata shi ne Maheerah ta dawo da ƙafarta gidan nan tunda bansan inda zan same ta ba."

Umma cikin kuka ta ce "Ka faɗa mata ta dawo don Allah muna buƙatarta, siyar da mutuncinta ba mafita ba ne a gare ta."

Ta yi zancen kamar wacce Irfan ɗin ya fadawa yana da hanyar yin magana da Maheerah a yanzu.

"Allah Ya maka albarka yaro ya baka Sa'a a tafiyarka, in dai ka samo ta na yi maka alƙawarin aura maka ita in sha Allah, domin ba za ta samu kamar ka ba."

Irfan ya amsa da Amin ya musu sallama sannan ya tafi cike da ƙwarin gwuiwa.

Washe gari tun da asuba ya ja akwatinsa ya bar gidan bayan ya yi sallama da iyayensa kuma ya nemi sanyawar albarkar su. Suka masa fatan samun nasara, kasancewar ya riga ya san hanyar garin kuma ƙwararre ne a tuƙi sai ya ja motarsa ya tafi da ita.

 

******

Sai da ya shafe sati biyu cur a jihar Balgori yana yawo club-club da gidajen masu zaman kansu a ƙarƙashin jagorancin abokinsa Umar, suna ta faɗi tashin nemanta amma ko mai kama da ita ba su gani ba.

Tafe suke a hanya Umar yana tuƙa mota kowannensu cikin yanayin damuwa.

Umar ya Dube shi ya ce "Ina ga wannan yawon ya isa haka, akwai wata hanya mafi sauƙi da zamu bi mu samu labarinta cikin sauƙi, in dai da kuɗi a hannunka."

Cikin zumuɗi ya ce "wace hanya kenan?"

"A ganina mu je gidajen talabijin na garin nan mu bada hotonta sannan mu saka kuɗi mai tsoka a kan duk wanda ya zo mana da labarin inda za a same ta."

Jikin sanyin jiki Irfan ya ce "wannan tunani naka na aiwatar da shi tuni, amma har yanzu ba labari."

Umar yana kallon titi ya ce "Ba a silar wannan ka samo labarin cewa tana nan garin ba? Yadda Hanif ya ganta a nan garin ba mamaki da yawa cikin makusantanta a yanzu sun gani. Idan suka ji labarin kyauta mai kauri yanzu za su zo maka da bayani."

 

Ba tare da dogon nazari ba ya amince da shawarar sannan suka miƙe hanya zuwa kai report ɗin ba a rufe sati ba sai da ya samu kira daga wata abokiyar harkallarsu cewa ta yi wa Maheeluv farin sani.

 

****

Mahee kuwa tun a ranar da ta samu labarin abin da ya faru da su Jafsee take cikin damuwa. Ta yi iya ƙoƙarinta a kan su Tukur su faɗa mata wajen ta je ta dubo halin da suke ciki amma sai suka ce su mata ba su tantance hanyar ba.

Har a zuciyar Maheerah ba ta ji daɗin abin da ya same su ba, don har ga Allah ba ta so wani abu ya taɓa lafiyarsu ba har su koma gida sai dai ƙaddara ta riga fata.

Tana cikin tashin hankali da taraddadi ta ji jiniyar motar 'yan sanda a layin su. Sosai take mamakin wanda aka zo kamawa a irin wannan hamshaƙiyar unguwar da kowa yake cin gashin kansa.

Ba wani wanda ya damu da rayuwar makwafcinsa bare ta yi tunanin wasu ne suka yi faɗa har labarin ya je kunnen jami'ai.

Sai dai ga mamakinta sai ta ji ana nocking ƙofar gidanta. Cikin hanzari ta fice daga falon lokacin daga ita sai wani wando tree querter da y'ar best ta shan iska sai 'yar hula kanta da yake ba ta jima da tashi daga bacci ba.

Tana buɗewa jami'ai biyu da ke sanye da kaki suka kutso kai cikin gidan.

Ɗayan ya nuna mata ankwa yana faɗar "You are under arrest."

Cike da mamaki take kallonsa "Arrest for what reason?"

Ya bita da kallon benen Wada "Ba mu zo nan don mu amsa miki wannan tambayar ba, idan mun je can kya ji."

Macer yar sanda ta karɓi ankwar ta saka mata suka iza ƙeyarta zuwa mota.

Ba yadda ba ta yi da su ba su mata uzuri ta sanyo suturar kirki suka ƙi sai ma baƙar maganar da macen ta yaɓa mata.

"Da ma aike ba 'yar mutunci ba ce tunda kike zaman kanki..."

 

 

 

Ummu Inteesar ce