ƘADDARA TA: Fita Ta 17

 ƘADDARA TA: Fita Ta 17


 ƘADDARA TA:


        Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 17*


                  ~Fita tayi da bala'in gudu kamar zata kife ɗakin ya kaseem ta nufa zata buɗe kenan ya fito zai tafi aiki, hanunshi kawai yaga ta riko cikin murna, yace "meeta meya faru?"
tana tsalle tace "muje ka gani"
janshi tayi yana binta a baya da kallon mamaki, ɗakinsu hameed suka shiga ta kaishi gaban hameed da yake zaune har yanzu yana zargin anya shine yayi magana?
tace "ya kaseem yarima ya fara magana"
kallon karya ne yayi mata, tace "wallahi da gaske"
kallon hameed yayi wanda yake binshi da ido, bai taɓa sanin Asmeeta batada hankali ba sai yau, yaune ya gama tabbatar da batada cikakken hankali yaranta yafi yawa akanta, tsaki yaja yace "shekaranki nawa?"
tayi shiru dan bata sani ba hamma najeeb ne ya sani, ya kalli hameed yace "hameed..."
yanaso ya karasa maganan yaji hameed yace "na'am"
with surprise yace "kamar naji kunnuwana sun min karya kamar magana naji kayi?"
ya jijiga kai yace "eh ya kaseem magana nayi"
zubewa kasa ya kaseem yayi ya kalli gabas yayi sujjada, hawaye yake yi cikin sujjadan yana godewa Allah, ɗagowa yayi yana hawaye suka rungume juna da hameed ɗin, duk cikinsu babu wanda ya iya kara yin magana, asmee da gudu ta fita taje ɗakin meenat, bacci take da karfi ta fara bubbugata cikin kasala ta buɗe ido tace "lafiya?"
tace "yarima ya fara magana"
sauka tayi a gadon ta fita daga ɗakin bata kara tambayanta ba, asmee binta tayi, fitowa sukayi shida ya kaseem tace "yaya yarima? da gaske ka fara magana?"
ya gyaɗa kai, cikin rashin yadda tace "ban yadda ba yaya kamin magana naji domin na tabbatar"
yace "meenat..?"
da gudu tazo ta faɗa jikinshi, sultan jin ihun da meenat take yi ya tashi a baccin da baiyi niyan tashi ba zuwa don duba meenat, gani yayi sun rungume juna da ya hameed, yace "meya faru?"
hameed cikin farin ciki yace "sultan?"
waro ido sultan yayi yace "yaya ka fara magana?"
da gudu shima yaje ya rungumesu, farin cikin da suke ciki kaɗai yasa meeta taji daɗi a ranta kamar family ɗinta take ganinsu, sultan ne yaje ya faɗawa Abi, tareda Ammi sukazo ya durkusa ya gaishesu, Abi ɗagoshi yayi ya rungumeshi ammi gabanta yana faɗuwa ta juya baya, kaseem ya kalleta zaiyi magana Aneeta ta shigo, kallonsu take da mamaki taɓe baki tayi zata wuce hameed yace "daga ina kike?"
wannan tambayan ya jima a ranshi kullum sai yayi mata wannan tambayan a zuciyarshi yaune Allah ya bashi dama da ikon furtawa, turus ta tsaya jikinta yana rawa, a razane ta juyo ta kare mishi kallo, Asmee gani tayi tana kallon hanunshi kamar akwai abinda take nema sai kuma ta kara kallon fuskanshi tace "ha..hameed?"
yace "eh nine daga ina kike?"
tace "naje karɓan passport ɗina ne"
buɗe jaka tayi ta nuna mishi passport ɗinta, ya kalla yace "okay"
cikin tsoro tazo tayi hugging nashi tace "congratulations"
yace "thanks"
sakinshi tayi tana musu murmushin rashin gaskiya ta tafi ɗaki, da kallo asmee ta bita, Abi yace "mun gode mun gode Asmeeta ki faɗamin me kikeso a rayuwarki koma menene na miki alkwarin zan baki koda rabin dukiyana kikeso zan baki"
murmushi tayi kanta kasa ta girgiza kai tace "bana bukatar komai Abi addu'a kawai nake bukata"
yace "Allah ya miki albarka"
tace "Ameen"
zata tafi yace "Asmeeta"
tsayawa tayi, yace "na ƴantaki daga baiwa kin zama me ƴanci daga yau ke ba baiwa bace a tare damu zaki fara zama"
cikin jin daɗi ta durkusa kasa tace "na gode Abi"
kaseem yace "ni kuma zan ɗauki nauyin karatunki zan saki a makaranta me kyau daga nan har kasar waje idan kinason karatu"
cikin girmamawa da jinshi tamkar hamma najeeb nata tace "na gode yaya na gode sosai"
sultan yace "ni kuma zaki zama kawata?"
murmushi tayi tace "eh"
meenat wacce taji sonta har cikin ranta tace "ni kuma zan baki kayan sawa masu kyau da tsada"
tace "na gode sosai"
ammi ce kaɗai batayi magana ba, kaseem yace "kije a ɗakin meenat zaku zauna kin zama ƴar gida"
ta kalli meenat dake mata murmushi ta mika mata hanu, sa hanun tayi a nata suka tafi, kallon Aneeta dake kallonsu ta tsagun kofan tayi, murmushin gefen baki tayi sannan tace "saina tona miki duk asirin da kike binnewa"
ɗakin meenat suka shiga, kaseem yace "ka kira alameen a waya ka faɗa mishi"
yace "to yaya"
yace "kuma tunda ka fara magana yanzu zaka fara asalin business daka saba wato harkan gold da diamond, nasan babu wanda ya kaika iya wannan harkan kap garinnan kuma zaka dawo kamar yadda ka saba Abdulhameed"
yace "insha Allah"
cikin farin ciki yace "company ɗinka da aka rufe za'a buɗe zaka fara aiki kamar yarima Abdulhameed na baya ba hameed na yanzu ba"
murmushi yayi yace "to yaya"
ammi ɗaki ta shiga tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un"
dafa kai tayi tana maimaita kalman.

washe gari ya kaseem ne ya sanar za'a buɗe company ɗin da aka jima da rufewa na ABDOOL DIAMOND COMPANY ya sanar da meenat su shirya itada Asmeeta da ita za'a tafi buɗe company ɗin da aka jima da rufewa, wani tsadadden bakin shadda wanda akayi ruwan stones a jiki ta bawa Asmeeta tace "shi zaki sa"
tace "anya zan iya sa wannan kayan? sunyi tsada"
tace "ya kaseem ne yace kisa"
tace "to"
shiri meenat ɗin tayi cikin shadda itama purple sunyi bala'in kyau itace ta karasa shirya Asmeeta wacce ta fito kamar balarabiyar amarya, fitowa sukayi Aneeta wacce tayi kyau itama cikin farin shadda fuskanta babu walwala ta kallesu kallo ɗaya ta watsar, duk ƴan gidan sun shirya harda ammi itama shadda tasa, Aneeta ta ɗaura alkyabba a saman kayanta, kaseem yayi bala'in kyau shima ya fito kamar balarabe, shiga ɗakin yayi ya gama fesawa hameed turare sannan yasa mishi alkyabban da yake sheƙi wanda kamar da gold akayi, sandanshi ya bashi yace "yau kowa zai san yarima hameed ya dawo"
murmushi yayi ya rungume ya kaseem cikin sanyin muryanshi yace "thank you yayana I love you so much"
shiru yayi jin zai fara kuka ya zameshi yace "zaka fara shagwaɓan naka ko?"
maida hawayen yayi ya rike hanunshi yace "muje"
fita sukayi me martaba tareda dogarayenshi suka fito yayi kyau cikin manyan kaya da naɗin sarauta dake kanshi, yace "masha Allah yarima na yayi kyau"
fita sukayi motocin da aka haɗa convoy sunfi hamsin, shiga na gaba sarki yayi tareda ammi da hameed da ya kaseem, Aneeta kuma da sultan da meenat da Asmee wacce tunda suka fito take attacking Asmeeta da ido, bata kalleta ba bale tasan tana kallonta.
sauran jama'a harma da bayin gidan suka shiga sauran motan kai tsaye aka wuce babban company ɗin hameed wanda tun ranan daya daina magana aka rufe yau kusan shekara da shekaru kenan, hawaye ya fara ganin hanyan company ɗin ya kaseem ne ya rike hanunshi yana mishi alaman kada yayi kuka, shima yana danne kukanshi har suka iso wani maƙeƙen company da yake da masifan kyau, daga sama an rubuta WELCOME TO ABDOOL DIAMOND COMPANY da rubutun da yake wuta yana haska wajen, shiga akayi dasu har ciki, an gyara komai tsofaffi ma'aikatanshi wanda rabonshi dasu har ya manta yana ganinsu kawai ya fara kuka, da kyar ya kaseem ya lallasheshi suka fito yana gyara mishi alkyabban, cikin jin daɗi sukazo suka rungumeshi harda masu kuka, kaseem ne ya basu hakuri suka karasa ciki, taro aka fara gudanarwa, Abi ya bawa hameed mic da kanshi yayi godiya wa mutane sannan ya nuna farin cikinshi na dawowa aiki.
office na hameed ɗin kujeran sarauta aka sa mishi komai na office ɗin ya tsaru babu abinda bai tsaru ba a wajen.

sai yamma likis aka tashi kowa ya koma gida, Asmeeta idonta akan Aneeta, ganin mutane suna busy yau a gidan yasa ta faki idonsu tabi ɗayan hanyan da tabi ranan asmee na binta har ta isa ta buɗe kofan, a fusace ta shiga asmee tana kallonta ta jima kafin ta fito tana huci ta rufe kofan, cikin sauri da fushin da take makullin ya faɗi bata kula ba, saida tayi nisa Asmee tazo ta ɗauki makullin ta wurgar da wani wanda ta tanada sabida wannan ranan a wajen, har Aneeta tayi nisa sai kuma ta duba hanunta taga babu makulli tsaki taja ta koma, ganin makulli tayi a hanya bata kula ba kawai ta ɗauka ta koma, cikin gida ta shiga tana maida fuskanta normal, Asmee dariyan farin ciki tayi tace "koma menene a wannan ɗakin kike ɓoyewa yau saina gani"
kashe jiki tayi ta koma cikin gidan hankali kwance ta ɓoye makullin da dare zataje ta buɗe taga me take ɓoyewa.
duk gidan farin ciki suke, meenat tana ganinta tace "Asmee kizo ki gaisa da wanda zan aura"
cikin rashin sakin fuska ta gaida alameen yayi mata godiya da taimakon abokinshi da tayi, ɗaki ta shiga tana kallon makullin.

cikin dare kowa yana bacci asmee cikin kayan baccin da meenat ta bata peach color ta sauka daga gadon makullin ta ɗauka ta saci wayan meenat domin kunna toci, fita tayi cikin sanɗa, dama tasan suna kashe wuta duk dare hakan yasa ta fita kai tsaye ta kofan baya da taga Aneeta tana fita ta can ta fita, cikin sanɗa take tafiya har ta isa wajen da yake lungu, babu me gane akwai ɗaki a wajen sai wanda aka faɗawa sai kuma wanda ya gani, makullin ta ciro saida ta juya taga babu me ganinta kafin ta buɗe kofan, cikin sanɗa take shiga duk da gabanta yana faɗuwa saida ta daure ta shiga, tun a bakin kofa ta fara jin wari, toshe hanci tayi ta kunna tocin wayar ta haska, kamar mutum ta gani a kwance kasa, kara haskawa tayi tace "mutum ne fa"
zuwa tayi ta kara haskawa rufe yake da bargo me bala'in datti bargon yayi baki ƙirin warin da yakeyi yasa ta gane yafi shekara baiyi wanka ba, abin mamakin ƙafarshi da hanunshi duk a ɗaure da bakin kaca (chain) ya duƙunƙune cikin bargon ko kanshi ba'a gani a waje, tace "to meyasa Aneeta ta kulleshi anan? me yayi mata?"
juyawa tayi tace "gara na tafi domin kamar baida rai"
zata tafi har taje bakin kofa taji yayi magana cikin murya me amo yace "ki buɗeni"
gabanta ya faɗi a razane ta kalleshi jin yayi magana, ya kara cewa "ki taimaka ki buɗeni banaso na mutu"
jikinta ya fara rawa tace "waye kai?"
yace "ni mutum ne kamar ke ba dabba bane ni ki buɗeni ina jin yunwa kuma banada lafiya karki tafi ki barni zan mutu"
ta kasa fita kuma ta kasa komawa ciki freezing tayi a wajen, jin kamar kuka yake tace "zan kawo maka abinci amma ba zan iya buɗeka ba domin ban san meyasa aka rufeka ba"
yace "to"
fita tayi daga wajen taje ciki Allah yasa babu kowa ta ɗauko abinci ta tafi dashi, kai mishi tayi tana tsoro ta aje mishi tace "tashi kaci gashi nan"
komawa baya tayi, tashi yayi kamar zaki a tsorace ta kara yin baya tana kashe tocin wayar sabida kada yasan inda take tsaye ya cutar da ita, abincin ya ɗauka sannan yace "ba zan iya ci ba hanuna a kulle yake"
tace "to ai babu makullin da zan buɗe wannan kacan dashi"
yace "makullin yana jikin wanda kika buɗe ɗakin dashi shine karamin"
ta kalli makullin hanunta ta haska da toci, ganin da gaske yake tace "kamin alƙawari ba zaka cutar dani ba"
yace "na rantse ba zan cutar dake ba"
a hankali taje ta durkusa a gabanshi buɗe kacan tayi da makullin jikinta yana rawa ta ɗaga tocin take tocin ya haska fuskanta, ta cikin bargon yake kallon kyakkyawan fuskanta murmushi ne ya suɓuce mishi rabonshi da murmushi tin ranan da aka kulleshi a wannan ɗakin sai gashi yau yayi sanadin kallon fuskanta, sai yaji kamar baya da wata damuwa a duniya ya kasa ɗauke idonshi akanta, tace "gashi"
kallon karamin bakinta da yayi magana yayi ta cikin hasken tocin, bata damu da taga fuskanshi ba, ya ɗaga hanu kamar zaici sai yaji hanun yayi nauyi yace "ba zan iya ci ba hanuna yayi nauyi kuma yana ciwo"
cikin tausayinshi da saurin da take tasa hanu ta ɗibi abincin ta kai bakinshi, a hankali ya buɗe bakin yana ci, saida ya koshi yace "na koshi"
muryanshi tsoro yake bata, ta tashi zata tafi taji ya damƙe hanunta, cikin rawan murya tace "dan girman Allah kada ka illatani kaga taimakonka nayi"
yace "ba zan cutar dake ba ina sanki"
zata kwace hanun ya tashi, baya tayi tace "dan girman Allah kada ka cutar dani"
dariya yayi sosai me amo sannan yace "karki damu jeki"
da gudun ceton rai ta fita a wajen bata damu da kulle kofan ko ɗaukan makulli ba.

_jiddah ce...
08144818849