Bai kamata a rika siyasantar da matsalaer tsaro ba----Sanata Tambuwal 

Bai kamata a rika siyasantar da matsalaer tsaro ba----Sanata Tambuwal 
 
Sanata Aminu Tambuwal ya bukaci ‘yan Najeriya da su marawa gwamnatin shugaba Tinubu baya wajen magance matsalar rashin tsaro, ya jaddada cewa bai kamata a rika siyasantar da matsalar tsaro ba.
 
Da yake magana a  ranar Asabar a Sokoto, tsohon gwamnan, yace rashin tsaro a Najeriya ba kadai na  shugaba Tinubu, jam’iyyar APC ba ne, na ksa ne gaba daya ba wata jam'iya ko  bangaranci ba,  batun tsaro makomar al’umma ne gaba daya. 
 
Tambuwal ya bayyana cewa, duk da cewa an samu cigaba, har yanzu akwai bukatar a kara himma wajen shawo kan matsalar, yana mai bayyana fatansa kan yadda za’a magance matsalar rashin tsaro a halin yanzu. 
 
Ya jaddada cewa rashin tsaro a Najeriya ba addini ba ne ko kabilanci, yana mai bayyana masu aikata laifin a matsayin miyagun gama-gari wadanda ayyukansu suka shafi 'yan Najeriya baki daya.
 
Sanatan ya kuma yi kira ga gwamnatin Amurka da ta sake duba matsayinta da kuma marawa gwamnatin Tinubu baya wajen tunkarar kalubalen tsaron kasar.
 
Tambuwal ya kara da cewa ta hanyar hadin gwiwa ne kawai za’a iya magance matsalar rashin tsaro, inda ya tuna cewa a lokacin da yake gwamna a karkashin marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari, an magance matsalar tsaro ba tare da bangar siyasa ba. 
 
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su tantance yanayin tsaro da idon basira tare da marawa duk wani yunkuri na maido da zaman lafiya da tsaro a fadin kasar.