DUHU DA HASKE: Fita ta ƙarshe
DUHU DA HASKE
Na
*Jiddah S mapi*
*Last Chapter*
~Biki Abba ya shirya me kyau da ammi, sabida suna so su yiwa yaransu gata, ɓangaren amare shiri suke sosai domin kuwa ameesha tana iya bakin kokari dan ganin ta shirya hanan da rayhana wacce a yanzu ta zama kamar ƴar uwarsu itama, komai tare suke yi, yau yake juma'a bayan sallan juma'a aka ɗaura auren rayhana da yazeed sai kuma hanan da faruk, ameesha ta zama busy haka ma ammi duk ba kansu, sai dare ammi tace itama tasa farin leshin da aka ɗinka musu domin itama yau zasu koma gidansu dukansu amare ne, lokacin da aka kusa tafiya Abba ya haɗasu gaba ɗaya yana musu nasiha, daga karshe ya fashe da kuka kawai ya kasa magana, ammi ma kuka take batason yaran suyi nesa da ita tafi son zamansu gida ɗaya amma ya zatayi? koba komai idan tayi kewansu zataje ta dubasu, sabida basu da nisa, Imran saida zasu tafi ya rike hanan yana kuka, abokiyar faɗanshi itace yafi jin kewanta, har suka fita suna kuka, rayhana a motar yazeed ita kuma ameesha a motar man sai hanan a motan faruk duk suka fita zuwa sabon gidansu da Abba ya musu kyautanshi, makotane gidan babu nisa ko kaɗan tsakaninsu, sun isa gida lafiya komai na gidan abin birgewa Abba yasa musu duk wani abin buƙata a gidan saide muce Allah ya basu zaman lafiya ameen.
******************
bayan wasu shekaru Ameesha ce ta fito daga mota tana rike da bulala karami a hanu, buɗe marfin motan tayi yara kanana kyawawa mace da miji suka fito, kowa yana share hawaye namijin yana kama da man sai macen kuma tana kama da ameesha, ta sasu a gaba suna tafiya har zuwa falon ammi, turo kofan tayi cikin tsawa ta ɗaga bulalan tace "ku shiga kafin na shoɗa muku"
shiga sukayi suna ganin ammi suka je da gudu, ammi tayi kyau sosai ta kara zama fresh tana sanye da dogon riga me kyau tasa mayafi akanta, siririn glass fari a idonta ta kalli yaran da suka rungumeta sannan ta kalli ameesha tace "me sukayi kika dake su?"
cikin gajiya da halinsu tace "ammi basu da aiki sai ihu, kinga me sunan umma tafi rashin ji itace take tsokananshi shi kuma saiya biye mata"
ammi tace "shine harda duka?"
zama tayi akan kerarren sofan dake ɗakin farin sal tace "zo nan yazeed ka daina biyeta kaji? kaga me sunanka baya faɗa kaima shiyasa ka zama baka faɗa karka kara biyeta kaji?"
yace "to granny"
zama ameesha tayi akan kujera tace "wai ammi babu abu me daɗi a gidanku ne?"
ammi murmushi tayi ta lura da yadda ameesha take yawan kwaɗayi a cikin ƴan kwanakinnan da alama tanada ciki, tace "akwai shiga ciki ki duba"
tashi tayi zata shiga ciki hanan tayi sallama, da gudu zaje suka rungume juna tace "yaushe a gari?"
hanan tace "yanzu saukanmu har munje gjdanku baku nan"
tace "amma kinyi kyau kinga yadda umara ya karɓeki kuwa?"
tace "Allah?"
ameesha tace "yes amma anya ke kaɗai ce? kinga yadda kike yin jiki?"
tace "ke ammi na nan fa"
Imran ya shigo yayi kyau sosai kuma ya ɗan manyanta ganin hanan ya saki fuska yazo ya rungumeta yace "Anty hanan yaushe kika dawo?"
tace "yanzu dawowa ta, kai kam meyasa ba zaka rage jiki ba? so kake ƴammata su kika ne?"
yace "ina ruwanki? ke da kikayi jiki waya miki magana?"
tace "sai kai"
yace "to dama sai ke ne"
ameesha tace "idan kun gama saiku zauna"
yace "Anty ameesha fahad fa yana can a school yana cin kwakwa wallahi exam suke na leka naga sai zufa yake"
dariya tayi tace "Allah bashi sa'a"
zama sukayi a falon suka fara zuba hira, ammi tace "rayhana ai bata jin daɗi cikin yana wahal da ita, kuma yazeed ɗinnan kamar baida hakuri duk yadda naso ta dawo wajena ta ɗan huta yaki saima kullum yana zuwa ɗakina saide naga yarinya bata sauki saima kara rashin lafiya kawai nace ta koma"
hanan tace "bari na kirata"
tana kira taji muryanta kasa kasa tace "sisi ya kike?"
hanan ta kalli ameesha sannan tace "ina lafiya na dawo ai yanzu ina gidan ammi tareda su ameesha"
da sauri tace "Allah? gani nan zuwa"
kafin tayi magana ta kashe wayan, da kyar ta tashi tana ciza baki ta kalli yazeed daya zuba mata ido tace "zanje gidan ammi"
taɓe baki yayi
"saikin dawo"
shagwaɓe fuska tayi tace "ka kaini"
yace "ba inda zanje"
komawa tayi ta zauna tayi shiru tayi tagumi, kallonta yayi haka kawai take bashi tausayi musamman idan yaga cikinta da yake bata wahala, yace "tashi muje"
murmushi tayi me kyau tace "na gode"
fita sukayi da kanshi ya kaita suka shiga tare, hanan da gudu tazo ta rungumeshi tace "yayaaa"
yace "kin dawo?"
tace "eh yaya"
rungume rayhana tayi tace "sannu da jiki"
da kyar tace "yawwa"
zama tayi a gefen ameesha ta gaida ammi shima yazeed ya zauna ya gaisheta kafin suka fara hiran tare, ya kira yazeed karami dake cinyan ammi yace "zo takwara"
zuwa yayi da gudu ya faɗa kanshi, hira ya fara yi dashi yana tambayan meya sameshi yayi shiru?
yace "momy ce ta dukemu"
harara ya aikawa ameesha sannan ya ɓata rai yace "me sukayi miki?"
tace "wallahi yaya kasan Allah basa jin magana"
yace "shine harda duka?"
tace "ayi hakuri ba zan kara ba"
man ne yaje gidan yaga babu kowa tama rufe kofa yasan tana gidan ammi gidan yazeed yaje akace mishi sun fita yasan suma can zasu je, motarshi ya shiga yayi kyau sosai fatarshi ta kara yin kyau akan nada, ga wani kwantaccen saje da yake fuskanshi, ya kara zama fari wannan karon hutu da kwanciyan hankali ya bayyana a jikinshi sosai, har ya isa gidan yayi parking sannan ya fito ya shiga ciki, a falo ya gansu, su yazeed karami suna ganinshi da moon me sunan umma sukaje suka rungumeshi, ya zauna kusa da ammi yace "Ammi jikokinki zasu karya ni yara sai karfi kaman uwarsu"
ameesha ta ɗago manyan idanunta tace "kamar ubansu dai"
dariya yayi yace "dama kin san na shigo kenan? amma babu ko sannu da zuwa"
tace "sannu da zuwa"
hira suka fara sosai, har dare suna gidan faruk tunda yaga bata dawo ba yasan sun gamu, shima da kanshi yazo domin su koma gida, ammi sai murmushi take tana kallon family ɗinta, Abba ya dawo tun daga bakin kofa yake jiyo muryansu yana shiga ya tsaya a bakin kofan falon yana rike da jakanshi da alama daga aiki ya dawo, ya kalli agogo ya kallesu kowa yana sunnar da kai sun san yanzu zai kaɗasu gida, yace "to me kuke jira har karfe tara?"
duk sukace "Abba ina wuni?"
yace "lafiya, kowa ya tashi ku kama hanyan gida, a bar yazeed karami da moon anan wajen kakarsu tunda sunyi bacci"
sum sum suka tashi kowa ya nemi jakanshi da mayafi suka yiwa ammi saida safe sannan suka fita, Abba yayi murmushi yace "Allah ya rayamin ku, Allah ya rabaku da mugun ido da mugun baki, kada Allah ya kawo me hali irin na manal koda a cikin ƴaƴanku ne, Allah ya nesanta mutum da mace kamar manal"
Ammi data karɓi jakanshi tace "ameen ya Allah"
_Tammmat bihamdi lillah anan na kawo karshen littafin duhu da haske, kuskuren dake ciki Allah ya yafemin, faɗakarwan dake ciki kuma Allah ya bani lada, to wani kalan labari kuke so na kara kawo muku ina nan ina jiran amsanku_
*Jiddah Ce....*
08144818849
managarciya