Bai Kamata ‘Yan Majalisunmu Suna Barin Abin Da Yake Hakkin Al'umma  Yana Wucewa Ba'a Yi  Ba------Dakta Balarabe Kakale Shuni

tabbas in mun tafi majalisa sai mun kalubalanci duk wata doka da ta zama karfen kafa ga cigaban al’ummarmu, misali harkar tsaro da ya tabarbare babu dalilin da zai hana a samar da dokar kafa ‘yan sanda mallakar jiha, na yi imani tsaro ba zai inganta yanda ake so ba, matukar kashi 100 na kulawar ‘yan sanda gwamnatin tarayya ke yi, a Nijeriya ana bukatar fiyeda ‘yan sanda miliyan amma yanzu ba su wuce dari hudu ba , akwai gibi na kusan miliyan guda, tsarin mulki da ya ce gwamnatin tarayya ke da alhakin tsaro yana da gyara don gashi yanzu karara an kasa. Tsari na lafiya da ilmin Nijeriya gaba daya suna bukatar garambawul, irin wannan abun ne za mu yi, abu ne na fatar baki za ka kawo a yi muhawara aba shi kulawa har ya zama doka.

Bai Kamata ‘Yan Majalisunmu Suna Barin Abin Da Yake Hakkin Al'umma  Yana Wucewa Ba'a Yi  Ba------Dakta Balarabe Kakale Shuni
Dr. Balarabe Kakale Shuni

 

Wannan wata tsohuwar hira ce da Dakta Balarabe Shehu Kakale ya yi   da Jaridar Aminiya kan takararsa da ya yi da dokar asusun kiyon lafiya da kirkiro da alfanunsa ga jama’a da sauransu. Mun wallafa ta ne domin muhimmancinta a wannan lokaci.

 

Aminiya:Dalilan da yasanya ka nemi takarar dan majalisar taraya  mai wakiltar Bodinga da Dange Shuni da Tureta

Kakale: Na gode Allah, dalilin da ya sanya na shiga siyasa har in shiga takara saboda zimmar ba da tawa gudunmuwa ga kiran da al’umma suka yi min. In jama’a suka ce ka ba da taka gudunmuwa bai kamata ka ki ba, musamman yankinmu da ke da kishirwar wakilci a haujin bunkasa kasauwanci da abubuwan more rayuwa da noma da ilmi da kiyon lafiya  a shekara 12 da ake waltarmu. A ganina in nasamu  dama zan yi tsaye a kwato hakkin yankinmu da kasarmu baki daya. Laifinmu ne da ke barin bara gurbi suna tafiya majalisa wakilci, dan majalisa ba yankinsa kadai fa yake wakilta  jiharsa ce gaba daya, in naje Sakkwato da Arewa zan wakilta, maganar da za ta taimaki mata da matasa da manoma da ‘yan kasuwa ita zan fi baiwa karfi, ba za mu bar abin da yake hakkinmu ya tafi ba.  Kuma akwai bukatar gyaran fuska na karfin iko da aka baiwa shugaban kasa ya yi yawa, a koma tsarin Firaminsta zai yi maganin bara gurbin wakillan da ake turawa, da suka zama cima kwance da dumama kujera, don a cikinsu za a rika daukar minista da sauran manyan mukaman gwamnati ka go ba mai yarda a tura wanda bai cancanta ba, balle ya tafi ba ruwansa da zaman majalisa sai dai a rika yi masa saynin na karya. Ni na yarda da a canja fasalin kasar nan, rashin canja fasalin Nijeriya yana cikin matsalolinmu a kasar nan, don wadan da ke yin aiki a Abuja ba su san matsalar jihohinmu  ba, aiki ya yi wa shugaban kasa yawa a gyara fasalin, kowane yanki ya yi mai fitar da shi, ba dalilin da zai sanya sai an dauki shanuwa mai rai an tafi da ita Lagas daga Sakkwato, a samar mata da daraja a rika gyara naman anan sai ka ga an samarwa matasa aiki, yakamata a sakarwa gwamnoni mara a tsarin samar da wuta su yi hulda da wasu kasashe su samu wutar lantarki mallakinsu, da harkar albarkatun ruwa, da sauransu, nauyi ya yiwa gwamnatin tsakkiya yawa.    

Aminiya:A duk lokacin da dan siyasa ya fito neman kujera za ka ji yana fadin zai kawo cigaba bayan ya samu nasara ba abin da zai kawo, kai wane madubi ne za a duba a ga ka bambanta da sauran masu fadi ba cikawa.

Kakale:To ni ba zan yi wa kaina alkalanci ba amma mutane sun san abin da nake fadi ko zan iya, abin da zan fadi nan a hulda ta da jama’a da sanin tarhina da ilmin da nake da shi na tabbata ina da rawar da zantaka ta neman hakinmu daidai da kundin majalisa, don wakilci ba abu ne da za ka zo ka shinfida hanyoyi ba, aikin majalisar zartarwa ne, aikin majalisar dokoki shinfida tsari a gudanarwar gwamnati da bibiyar aiyukkan gwamnati da suka shafi al’ummarka. Tarnaki da Nijeriya ke fuskanta ya ta’allaka ne ga dokoki da tsarin da ake ciki wasunsu sun tsufa ba su tafiya da zamani, tabbas in mun tafi majalisa sai mun kalubalanci duk wata doka da ta zama karfen kafa ga cigaban al’ummarmu, misali harkar tsaro da ya tabarbare babu dalilin da zai hana a samar da dokar kafa ‘yan sanda mallakar jiha, na yi imani tsaro ba zai inganta yanda ake so ba, matukar  kashi 100 na kulawar ‘yan sanda  gwamnatin tarayya ke yi, a Nijeriya ana bukatar fiyeda ‘yan sanda  miliyan amma yanzu ba su wuce dari hudu ba , akwai  gibi na kusan miliyan guda, tsarin mulki da ya ce gwamnatin tarayya ke da alhakin tsaro yana da gyara don gashi yanzu karara an kasa. Tsari na lafiya da ilmin Nijeriya gaba daya suna bukatar garambawul, irin wannan abun ne za mu yi, abu ne na fatar baki za ka kawo a yi muhawara aba shi kulawa har ya zama doka. Don kasan abin bana wasa ne ba, anan Sakkwato mun ba mai girma gwamna shawara kan maganin Mura wanda yake dauke da Kodin, a duk kasar nan mu muka fara jerengwano na neman gwamnatin tarayya ta hana shigowa da shi, muka yi kasidu da tarukka, muka hada kai da sashen soja aka rufe wurin sayar da kwaya a kasuwar sojoji Mami, bayan rubuce-rubucen sanar da jama’a wannan maganin guba ce ga al’ummarmu da taro a Kano da Lagas a karshe gwamanti ta ji kiran Sakkwatawa, duk da haryanzu akwai sauran aiki.

Aminiya: Abubuwan da kake ganin yakamata a yiwa gyaran fuska akwai sha’anin lafiya a matsayinka na kwararren likita a fannin lafiya ya kake kallon tallafin asusun tattara kudi na gwamnatin tarayya da badakalar da ake zargin ana tafkawa a cikinsa.

Kakale: Farfesa Yusuf ya zo da niyar gyara amma an ki barinsa ya aiwatar da abin da ya dace aka sanya masa tarnaki aka lalata abin har aka dakatar da shi. A haka sai gwamnatin Tambuwal ta fito da asusun wakafi  na lafiya, abin da ake so a Sakkwato a samar da baitil mali ta kula da maras lafiya don rashin lafiya ba ta baka lokaci kwatsam take zuwa musamman manyan rashin lafiya da ke sanya a sayar da gida ko gona ko jalli ya kare, ire-iren ciyon kamarsu Koda da Daji  da  ciwon lakka da hawan jinni mai tasanani, a kididigarmu jihar Sakkwato baki daya masu ciwon ba su kai dubu 10 ba, wannan tsari zai sa gwamnati da al’umma su dauke masu wahalar magani, a wani kiyasi namu a jihar  maras lafiya ba za su wuce dubu 150 ba, a cikin mutum milyan biyar da muke da su, a kalla in an ka samu mutum miliyan daya na sanya kudinsu a hada dana gwamnati a Sakkwato maras lafiya zai samu gata, zai zo da katinsa ne kawai a sibiti aba shi magani daga kan  maleriya zuwa dashen koda ba tare da ya biya ko kwabo ba, amma kafin haka sai mutum ya rika zubi na wakafi. Wannan shirin mun kwaikwayi gwamnatin tarayya ne muka yiwa namu gyaran fuska ya dace da abin da musulunci ya aminta da shi don kawar da aringizo da gibi, muka kaucewa maganar Inshora wadda take haramun ce a musulunci don ta ci karo da shari’a, akwai Garar tsanin rashin tabbas, da Maisir caca, da Riba ruwa, da maganar mata guda da diya hudu, da nuna wariya ga marasa lafiya  duk mun yi wa wadan nan kwaskwarima yanda addini ya aminta, mai karfi ya taimaki mai rauni, mai lafiya ya taimaki maras lafiya shi ne amfanin asusun bayan albarkar taro da kara inganta tattalin arziki a jihar. Wannan shirin za a kaddamar da  shi kuma za a samu amfanin shi.