ANA BARIN HALAL..: Fita Ta 17
ANA BARIN HALAL..:
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
*PAGE* 17
Tunda muka samu wurin zama muka zauna maryam da hadiza suke ɓaɓɓaka dariya, gaba ɗaya haushin su ya kamani, don na rasa me yake saka su dariyan, ɗaure fuska nayi naja tsaki nace, " amma dai za kusa a raina mu irin wannan dariyan ƙauyancin da kuke yi, tou meye ne ma kuke wa dariyan"? Na faɗa ina hararan su, kaman wani jira suke nayi magana sai suka sake kwashewa da wani dariyan, wanda har suka saka fatima ma ta ɗan dara, tana kallon su tace, "haba ku kuwa ku daina dariyan nan mana ae zaku saka ido ya dawo kanmu, gashi ma yanzu na hango Aunty b ta wani tsura mana ido,"
Sokaye ne ae na faɗa ina ƙara hararan su, dai-dai lokacin DJ ya isar da saƙon shigowan ango da amaryah, dole suka tsagaita da iskancin dariyan nasu muka maida hankalin mu kansu, ango da amaryah ne a gaba, bayan amaryah jerin friends ɗinta ne, bayan ango ma jerin friends ɗinshi ne, wato ko wani aboki yana jere da ango.
Sulaiman da yusuf sune asalin abokan yayah Ahmad wanda suka taso tare tun primary, kuma an taso dasu anguwa ɗaya, da babu abunda yake rabasu dare da rana, yanzu ne kowa aiki ya banbanta musu garin zama, sai haɗuwan su ba irin da ba, sulaiman da yusuf duk sunyi aure kusan shekaru biyu baya, saboda auren su babu nisa a tsakani, kuma ko yanzu sune jagaba a hidiman, don bayan ango sulaiman ne, sai A.G, bayan A.G kuma yusuf ne, sai wani abokin shi nura babah, sai M.G sai wasu da bawani zuwa sosai sukeyi ba, ido na yana kansu har suka ƙarasa wurin zaman su, gaskiya matar yayah Ahmad mai kyau ce masha Allah na faɗa a zuciyana, high table ɗin ango ne kawai da amaryah a zaune, suna rakasu suka koma wurin zamansu suka zauna, gefe ɗaya amare ɗaya gefen angwaye.
Babu ɓata lokaci aka fara programm ɗin, inda aka ƙira babban yayah mohd ya buɗe taro da Addu'a, sannan aka ƙira babban abokin ango wato sulaiman ya bada tarihin ango, abun gwanin burgewa ya bada tarihin shi cike da burgewa da ilimi, yana gamawa wuri ya kaure da tafi, da yake saida ya gama yi mishi iya shege a ƙarshe wanda yasaka kowa a hall ɗin darawa, ina ganin yayah Ahmad bini-bini yana sunkuyawa kunnen amaryah yana mata magana, gaba ɗaya mamakin shi ya cika ni, dama yana sakewa haka? Sai wani murmushi yakeyi wanda yaƙi barin fuskan shi, bayan ƙawar amaryah ta bada tarihin ƙawarta sai aka fara abun da ya tara kowa, fili aka baje wa ango da amaryah domin rawa, fitowar su aka saka musu waƙan *ALI JITA* na amaryah da ango, haba zokiga abokan ango yadda suke baza naira kaman basu so, ina hango Nura Baba sai naji ɗan tausayin shi, domin yanuna yana son habiba har yayiwa yayah Ahmad magana lokacin zamu fara rubuta exams na SSCE, sai yayah yace yayi wuri yayi maganan ya bari sai ta shiga university, shima lokacin yana shirin tafi UK masters ɗin shi, har Yaya Ahmad ya ƙirani agaban Nura Baba ya tambayeni akwai wanda habiba take kulawa ne ko sukayi maganan aure da shi, a lokacin nace mishi bamu kula kowa dukkan mu, ya juya ya kalli Nura yace kaji abunda nagaya maka ko? Yaran nan basu fara zance ba, amma insha Allahu na maka alƙawari suna farawa zan maka magana, Nura ustaz ne shi ɗan sarauta ne me kuma sanin ya kamata, yana da kirki da zumunci sosai, kallo na yayi yace, "sister amana yana hannun ki, ki kula da ita kada kibarta ta kula kowa, ke kuma nasan gudumawanki na tsaro da zan baki," ya faɗa yana dariya ni da yayah Ahmad ma dariyan mukayi, sannan ya kwaɓe ni da kada nagaya mata, amsa mishi nayi akan bazan faɗa ba amma nasan bazan iya riƙewa ba, a wurin na tafi na barsu suna ta zanta maganan tafiyan Nuran, sai da mukazo kwanciya bana mantawa ina ta kallon habiba da take gyara mana wurin kwanciya ni kuma ina shiryah mana books ɗin da mukayi karatu ina ta murmushi, gajjiya tayi da kallon da nake mata tace, "sisto akwai wani jarida ne kam"? Dariya na kwashe da shi nace, " amanatul amana, azabatul axaba, dariya muka kwashe da shi don tare muka ƙarasa faɗa, yawanci idan ɗaya zatayi wa ɗaya gulman da aka kwaɓeta haka mukeyi, kamo hannu na tayi muka koma bakin gadon muka zauna, Bayani dallah -dallah na mata, ina gama gaya mata ta wani zaburo ta dafah ƙirji tace, "ustaz nura baba"? Ɗaga kai nayi alaman ehh, fuskana ɗauke da murmushi, rungume ni tayi tace , "Alhmdllh sisto, gaskiya naji daɗin wannan jaridan, kuma nutsuwar shi yana burgeni, matsalar ɗaya ne, ni guntuwa shi guntu, amma duk da haka babu matsala yaran zasuyi kyau masha Allah, kinsan ni bana son farin mutum, gashi nuru ba fari bane irin kalan mijin da nake so", hararan ta nayi cikin wasa nace , "yarinya baki da wayo, ae farin mutum duniya ne, yarinya miji ya tashi a bacci kiga farin jiki ae duniya ne, amma baƙin fata nayi juyi cikin dare nayi arba da baƙar cinya ae razana zanyi", na faɗa muna kwashewa da dariya, habiba ta kaimun duka a cinya.
Lokaci guda naji kewan habiba yazo mun, abun yana mun ciwo yanzu duk irin wannan ƙauna da shaƙuwan da yake tsakanin mu habiba ta yarda akan namiji muka rabu? Muryan maryan naji akaina tana cewa, "ke matar farare ana ƙiran familyn ango a fili, ke kuma kin tafi duniyan tunanin waye dai a ciki oho", ta ƙarasa faɗa tana dariya, hararan ta nayi na miƙe domin muje filin, don gaba ɗaya idon yayah umar yana kaina, ina cewa bazan fito ba zaizo inda nake, dama yayi mun warning agida, ko bazanyi rawa ba ya ganni a fili.
Muna fitowa aka sako mana waƙan Ali jita, haba zokiga su fatima da su hafsy, maryam ummitah, hadiza yadda suke chashewa, Aunty b sai chashewa takeyi yayah mohd yana dubanta fuska ɗauke da murmushi, liƙi yafara kaman ba gobe, dangin mu na gefen ummi da Abba duk sun fito, fili ya kachame da ruwan kuɗi, ballan tana da yayah umar da yayah ishaq suka kamo hannun ango suna liƙa mishi kuɗi suka shigo da shi fili, ae gaba ɗaya abun sai ya baɗa cittah da unga, Aunty Asma'u, Adda, Aunty b da mu duka muka fara mishi liƙi, yayah umar ya riƙe hannun shi yana rawa, abun mamaki dayawa kawai sai ga yayah Ahmad yana wani chashe rawa, ae dukkan mu muka hau ihu ana liƙa mishi kuɗi, Yayah mohd yana dariya ya jawu su dukkan su ya rungumesu, muma mukaje muka rungumesu nida hafsy, *AUNTY NICE* sai da naji hawaye yazo mun alokacin, domin yadda naga wani farin ciki da ƙaunan juna a fuskan mu duka, Aunty B sai video take mana ita dasu maryam da su ummitah, domin hattah hadiza da zainab yayah mohd ya rungumu su, Adda har wahaye ta fara lokacin da yayah Ahmad ya riƙo ta ita da Aunty ma'u yana rawa da su, kai zumunci akwai daɗi, Allah ka ƙara haɗa kanmu baki ɗaya, haka muka cinye lokacin mu kowa ta koma wurin zama, anan DJ ya sake gayyati familyn amarya, suma suka fita suka chashe nasu.
Bayan ƙawaye da amaryah sun fito sun chashe, mun musu liƙi sosai, sai aka ce amaryah ta tsaya a fili ita kaɗai, sannan ango yazo ya nuna mata irin ƙaunar da yake mata, wurin yayi tsitt, fitowan ango yazo ya tsaya gaban amaryah ya ƙura mata ido yana wani binta da kallo fuskan shi ɗauke da murmushi ita kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa, sautin waƙan *ALI JITA* kawai yake tashi a hankali, inda yake raira waƙan
managarciya