Yadda zaki gyara fuskar ki da Garin Dabino
Yadda zaki gyara fuskar ki da Garin Dabino
Daga Maryam Ibrahim.
Ƴar uwa ko kinsan yadda zaki gyara fuskar ki ta dinga sheƙi na musamman da garin Dabino? Idan amsar ta kasance "a'a" to ta hanya mai sauƙi zaki sami shaiƙin fuska, dana hasken fuska, mai ban mamaki cikin kwanaki ƙalilan.
•Dafarko zaki tanadi garin Dabinon ki, sai zuma da man zaitun. Ki haɗesu a wuri ɗaya ki cakuɗe. Idan kin tabbatar da garin ya garwaya da zumarki da man zaitun ɗin ki, sai ki shafa a fuska. Ki ba shi awa ɗaya, sai ki sa ruwan ɗumi ki wanke fuskarki.
Sai an gwada.....!