Deprecated: Return type of LayerShifter\TLDExtract\Result::offsetExists($offset) should either be compatible with ArrayAccess::offsetExists(mixed $offset): bool, or the #[\ReturnTypeWillChange] attribute should be used to temporarily suppress the notice in /home/smmdrkqs/managarciya.com/application/third_party/domain-parser/layershifter/tld-extract/src/Result.php on line 189
Deprecated: Return type of LayerShifter\TLDExtract\Result::offsetGet($offset) should either be compatible with ArrayAccess::offsetGet(mixed $offset): mixed, or the #[\ReturnTypeWillChange] attribute should be used to temporarily suppress the notice in /home/smmdrkqs/managarciya.com/application/third_party/domain-parser/layershifter/tld-extract/src/Result.php on line 203
Deprecated: Return type of LayerShifter\TLDExtract\Result::offsetSet($offset, $value) should either be compatible with ArrayAccess::offsetSet(mixed $offset, mixed $value): void, or the #[\ReturnTypeWillChange] attribute should be used to temporarily suppress the notice in /home/smmdrkqs/managarciya.com/application/third_party/domain-parser/layershifter/tld-extract/src/Result.php on line 251
Deprecated: Return type of LayerShifter\TLDExtract\Result::offsetUnset($offset) should either be compatible with ArrayAccess::offsetUnset(mixed $offset): void, or the #[\ReturnTypeWillChange] attribute should be used to temporarily suppress the notice in /home/smmdrkqs/managarciya.com/application/third_party/domain-parser/layershifter/tld-extract/src/Result.php on line 267
Deprecated: Constant E_STRICT is deprecated in /home/smmdrkqs/managarciya.com/system/core/Exceptions.php on line 75
A PHP Error was encountered
Severity: 8192
Message: Creation of dynamic property CI_DB_mysqli_driver::$failover is deprecated
Filename: database/DB_driver.php
Line Number: 371
Backtrace:
File: /home/smmdrkqs/managarciya.com/application/config/config.php
Line: 338
Function: DB
An gano dalilan da suka sa aka dage sauyin sheƙar Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, zuwa jam’iyya mai mulki ta APC, bayan an riga an kammala shirye-shirye na farko.
A ranar Juma’a, jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa gwamnan ya kammala shirye-shiryen sanar da sauyin jam’iyyarsa zuwa APC a ranar Litinin.
Kafin a dage batun sauyin jam’iyyar, hedikwatar jam’iyyar APC ta ƙasa ta shirya cewa gwamnan zai zama mutum na farko da za a yi wa rajista a Kano a sabon tsarin rajistar yanar gizo na jam’iyyar.
Bisa tsarin da aka fara tsara wa, tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ne zai raka gwamnan zuwa mazabarsa ta Diso domin yin rajista a shafin yanar gizon jam’iyyar tare da karɓar katin jam'iyya.
Bayan kammala rajistar gwamnan, an shirya cewa nan take zai raka Ganduje zuwa garinsa na asali a karamar hukumar Dawakin Tofa domin sabunta rajistarsa a sabon shafin yanar gizon jam’iyyar.
Sai dai wasu majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya bayar da umarnin a dakatar da sauyin shekar ta Abba har sai an yi ƙoƙari wajen shawo kan uban gidansa na siyasa, Rabiu Kwankwaso.
A cewar majiyoyin, shirin Kwankwaso na sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC ya sauya lissafin APC.
“Fadar Shugaban Ƙasa na da bayanan sirri cewa Kwankwaso ya gana da Obasanjo da Peter Obi, kuma akwai yiyuwar su haɗa kai domin kalubalantar Tinubu a 2027. Tikitin Obi/Kwankwaso haɗin gwiwa ne mai ƙarfi da zai iya sauya ma’aunin siyasar APC.
“Kuma idan babu Kwankwaso, ƙarfin siyasar gwamnan zai ragu. Saboda haka Tinubu na sake tunani kan sauyin jam’iyyar Gwamna Yusuf.
“A gaskiya ma, gwamnan ne ke neman shiga APC, ba APC ke nemansa ba. Shi ya sa har yanzu babu cikakkun sharudda kan wa zai samu wani abu a cikin rabon madafun iko bayan sauyin jam’iyyar gwamnan,” in ji wata majiya.
Sai dai wasu majiyoyi sun shaida wa wannan jarida cewa gwamnan da kansa ne ya nemi ƙarin lokaci domin ya samu damar shawo kan ƙarin mambobin Majalisar Dokoki ta Jiha da ta Ƙasa su bi sahunsa wajen sauyin jam’iyyar.
Wasu majiyoyi da ba a tabbatar da su ba sun kuma shaida wa wannan jarida cewa matsin lambar da gwamnan ke fuskanta ta sanya shi cikin ruɗani, har ta kai ga yana tunanin janye batun sauyin jam’iyyar tare da komawa ya sake haɗewa da uban gidansa Kwankwaso.
Hakazalika wasu majiyoyi na cikin gida sun tseguntawa DAILY NIGERIAN cewa an dakatar da wannan shiri ne bayan an ja hankalin gwamnan kan bukatar ya fara ganawa da manyan shugabannin APC a Kano, musamman Abdullahi Ganduje da Sanata Barau Jibrin, domin neman albarkarsu kafin ya sanar da sauyin jam’iyyar.
“Idan gwamnan ya sauya sheƙa ba tare da ya gana da Ganduje, Sanata Barau da sauran shugabannin APC ba, zai nuna kamar yana raina su. Kuma hakan ba zai yi masa kyau ba,” in ji wata majiya da ke da masaniya kan lamarin.
Ko da yake DAILY NIGERIAN HAUSA ta rawaito rahoton jaridar Platinum Post cewa gwamnan zai sanar da sauyin jam’iyyar a ranar 12 ga Janairu, wasu majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa wannan ranar ba tabbatacciya ba ce, kuma sauya shekar na iya faruwa “a kowace rana bayan ya gana da shugabannin APC na Kano.”