APC ta fara zawarcin Gwamnonin PDP guda biyu

APC ta fara zawarcin Gwamnonin PDP guda biyu

APC ta fara zawarcin Gwamnonin PDP guda biyu

Jam'iyar APC mai mulki a Nijeriya ta fara zawarcin gwamnonin adawa guda biyu jigon jam'iyar a kasa Kashim Ibrahim Imam ya sanar da hakan cewa sun fara zawarcin gwamnoni PDP biyu su dawo jam'iyarsu .
Duk bai fadi sunayen gwamnonin ba amma ya tabbatar da tsohon gwamnan Oyo Alhaji Rashidi Lodoja nan ba da jimawa ba zai shiga jam'iyarsu.

A firar da aka yi da shi Imam wanda yake tsohon dantakarar gwamnan Borno ne a PDP sau biyu kafin daga baya ya koma APC ya ce wasu gwamnonin PDP za su dawo APC nan ba da jimawa ba, ya ce wannan cigaba ne sosai ga kasa.
Haka kuma kan maganar baiwa Igbo takara shugaban kasa a 2023 ya ce sun cancanta a ba su amma da wahala APC ta ba su domin yankinsu jam'iyar ba ta karfi a can.

Sakataren yada labarai na PDP Kola ya ce gwamnoninsu da suka hadu a wurin taro sun tabbatar ba wanda zai barin jam'iyar.