Na Kirkiro Cibiyar Koyar Da Mata Sana’o’in Hannu Ne Don Na Kawar Da Zaman Banza A Tsakaninsu----Dakta Larai Aliyu Tambuwal

"Cibiyar ta yi rijistar mata kusan 400 ana koyar da matan dunki da yin kayan kamshi na jiki da daki da man dakin da sauran kayan kamshi.  "A kwanan nan ne muka yaye mace 150 da suka koyi yanda ake hada kayan kamshi da wasu 50 da suka koyi dunki dukansu mun raba musu kayan da suka koya don dogaro da Kai." a cewar Dakta Larai.  Ta ce cibiyar kwalliya ta biya kudin sabulu, mafiyawan wadan da suka koyi Sana'ar a yanzu suna cin amfaninta musamman masu yin kayan kamshi, suna kai hajojinsu a kasuwannin kauye da gidajen matan aure kuma suna samun abin kashewa daidai gwargwado.  "Don su kara rike sana'o'insu muna gabatar masu da kasidodi a lokacin horaswa. Muna kai gudunmuwa ga matar da ta samu haihuwa da raba kayan masarufi a farkon watan Ramadan da sayen kayan masarufi don neman riba a gaba.

Na Kirkiro Cibiyar Koyar Da Mata Sana’o’in Hannu Ne Don Na Kawar Da Zaman Banza A Tsakaninsu----Dakta Larai Aliyu Tambuwal

 

Dakta Larai Aliyu Tambuwal likita ce da ta assasa cibiyar koyar da mata sana’o’in hannu a gidanta dake unguwar Nakasarin Ardo  a karamar hukumar Sakkwato ta kudu a jihar Sakkwato watan Junairun shekarar 2019.

Dakta ta samar da kayan amfani a cibiyar irinsu Teloli da kayan amfaninsu da sinadaran hada man shafi da sabulu man wankin kai da kayan kamshi a cibiyarta dake karkashin kungiyar matan Nakasari(NAWARDA), kungiya ce da aka kirkiro don tallafawa kai tsakanin mata da yin zumunci tsakanin mambobi da wayar da Kai dangane da lamurran yau da kullum da ilmantar da juna game da zamantakewa ta da kiyon lafiya da koyar da sana'a don rage zaman banza tare da karfafa dogaro da Kai da warware matsalolin da suka shafi addinin musulunci da kuma kulawa da lafiyar mata da kananan yara da matasa ta hanyar nema musu kariya daga cuta, ba da hakki na tarbiya, abinci da sutura da hana zaman banza da shaye-shaye da abin da suke haifarwa.

Dakta Larai Aliyu Tambuwal a zantawarta da Managarciya   ta ce ta kirkiro cibiyar koyar da mata sana'o'in hannu ne don ta kawar da zaman banza a tsakaninsu.

"Cibiyar ta yi rijistar mata kusan 400 ana koyar da matan dunki da yin kayan kamshi na jiki da daki da man dakin da sauran kayan kamshi. 

"A kwanan nan ne muka yaye mace 150 da suka koyi yanda ake hada kayan kamshi da wasu 50 da suka koyi dunki dukansu mun raba musu kayan da suka koya don dogaro da Kai." a cewar Dakta Larai. 

Ta ce cibiyar kwalliya ta biya kudin sabulu, mafiyawan wadan da suka koyi Sana'ar a yanzu suna cin amfaninta musamman masu yin kayan kamshi, suna kai hajojinsu a kasuwannin kauye da gidajen matan aure kuma suna samun abin kashewa daidai gwargwado. 

"Don su kara rike sana'o'insu muna gabatar masu da kasidodi a lokacin horaswa. Muna kai gudunmuwa ga matar da ta samu haihuwa da raba kayan masarufi a farkon watan Ramadan da sayen kayan masarufi don neman riba a gaba.

"Mun fito da cibiyar ne a yunkurinmu na  son a rage dogaro da gwamnati kacokam komi sai ta yi, ka dai yi iya naka sai gwamnati ta tallafa,  masu hannu da shuni su rika shiga cikin irin wannan halin su saka jari yana da kyau, in mazaje suka ba da hadin Kai mata za su rage masu wani nauyi dake saman kansu don tallafawa juna, bukatarmu wadan da muka horas kar su yi wasa don samun alheri a cikin rayuwarsu."in ji Dakta Aliyu Tambuwal.