Atiku Ya Yi Alkawarin Bude Dukkan Bododin Nijeriya Domin Shigo Da Kayan More Rayuwa

Atiku Ya Yi Alkawarin Bude Dukkan Bododin Nijeriya Domin Shigo Da Kayan More Rayuwa

 

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kadan daga shirinsa idan aka zabe shi a zaben 2023. 

Atiku ya bayyana cewa, yana da nufin bude iyakokin kasar nan domin ci gaba da shigo da kayayyaki sabanin yadda gwamnatin APC ta yi. 
Ya bayyana hakan ne a filin wasanni na Muhammadu Dikko da ke Katsina, kwanaki 66 kafin zaben 2023. 
Da yake jawabi, Atiku ya yi alkawarin cewa, zai magance matsalolin tsaro kana ya inganta tattalin arzikin kasar nan. 
Hakazalika, batun yajin aikin malaman jami'a, Atiku ya ce zai tabbatar da ya biya musu bukatunsu tate da warware dukkan matsala. 
A cewarsa: "Duk wani cigaba da kuke gani a Katsina, an samar dashi ne a mulkin PDP ciki har da wannan filin wasan, da ma sabon gidan gwamnati."