Yawaitar Cin Awara A Tsakanin Al'ummar Hausawa Yunwa Ko Marmari?

Sanin kowa ne kudade sun yi ƙaranci a hannun jama'a, kuma gashi muna bukatar abinci don mu rayu domin kuwa Sai da ruwan ciki akan ja na rijiya dalili kenan da ya sanya cin awara ya yawaita a yanzu. Muhammad Kabiru yana ganin cin Awara a wannan lokaci Marmari ne kawai domin ba ya cikin tsarin abincin da mutum ke ci ya koshi yakan tallafawa mai jin yunwa ne kafin ya samu abinci da yake da nauyi, "ni dauki cinsa a matsayin marmari ne kawai, don a duk sanda nake jin yunwa ba zan tunkarin cin awara ba,"a ceawar Kabiru. Nusaiba Shehu a nata tunanin cin awara marmari ne kawai ba zancen yunwa a cikinsa, layi daya na dauke shi da shan shayi in da hali  a yi in ba hali a bari, 'Awara ba tuwo ne ba ana cinsa ne kawai don marmari da bukatar sauya abinci in ya zo,' a cewarta

Yawaitar Cin Awara A Tsakanin Al'ummar Hausawa Yunwa Ko Marmari?

 

Shin marmari ne ke janyo cin AWARA ko kuwa  yunwa ce?

 

A shekarun baya akasarin waɗanda suke cin AWARA (ƙwai-da-ƙwai) suna ci ne don marmari ko kwaɗayi, kamar yadda mutane masu yawan shekarru suka bayar da labari ga Managarciya.

Sun ce  wancan lokacin ba ma ko'ina ake siyar da shi ba, sai dai in kun yi ra'ayi ku yi a gida ku ci, sabanin yanzu da kusan ba wani lungu da sako da baka samu masu girka tunkiyar soya shi ba, an samu yawaitar masu siyar da AWARA sosai fiye da baya. Ita  abinci ne  da za ka iya siya da karancin kuɗi kuma ka ci ka koshi.

 

Sanin kowa ne kudade sun yi ƙaranci a hannun jama'a, kuma gashi muna bukatar abinci don mu rayu domin kuwa Sai da ruwan ciki akan ja na rijiya dalili kenan da ya sanya cin awara ya yawaita a yanzu.
Muhammad Kabiru yana ganin cin Awara a wannan lokaci Marmari ne kawai domin ba ya cikin tsarin abincin da mutum ke ci ya koshi yakan tallafawa mai jin yunwa ne kafin ya samu abinci da yake da nauyi, "ni dauki cinsa a matsayin marmari ne kawai, don a duk sanda nake jin yunwa ba zan tunkarin cin awara ba,"a ceawar Kabiru.
Nusaiba Shehu a nata tunanin cin awara marmari ne kawai ba zancen yunwa a cikinsa, layi daya na dauke shi da shan shayi in da hali  a yi in ba hali a bari, 'Awara ba tuwo ne ba ana cinsa ne kawai don marmari da bukatar sauya abinci in ya zo,' a cewarta.
Mudassiru Auwal yana ganin cin awara da ake yi a lokacin la'asar da magrib yunwa ce ke sanya haka, "kai kasan duk wanda ya tafi sayen awara ka san yunwa yake ji kuma ba ya da kudin da zai je ya sayi babban abinci ya ga bari ya tsaya, a wurin  da yake da zarafi don ya koshi cikin lumana.
"Domin an san yanzu an mayar da shi abincin yunwa baka masu sana'ar sun yawaita ba tare da fitowa salo kala-kala don inganta abincin a dai ci a koshi", in ji shi.  

Daga Rukayya Ibrahim Lawal Sokoto