Zan Ba Da Gudunmmuwata Sosai Don Ganin Yankina Ya Samu Cigaba----Sanata Ibrahim Lamido

Zan Ba Da Gudunmmuwata Sosai Don Ganin Yankina Ya Samu Cigaba----Sanata Ibrahim Lamido

Zababban Sanata a yankin Sakkwato ta Gabas Sanata Ibrahim Lamido  ya kara tabbatar da kudirin da yake da shi na ciyar da yankin Sakkwato ta Gabas a gaba kamar yadda ya alkawanta a farko.

 Sanata Lamido shi da jam'iyarsa ta APC sun samu nasarar lashe zaben da hukumar zabe ta gudanar, ya samu kuri'a dubu 112,764, in da ya kayar da abokin takararsa na jam'iyar PDP Shu'aibu Gwanda Gobir wanda ya samu kuri'a dubu 107,834.

Lamido bayan aiyana zabensa ya godewa dukkan mutanen yankin Sakkwato ta gabas musamman magoya bayansa da suka yi tsaye don tabbatar da wannan nasarar ta samu, a cigaba da rokon Allah don cigaba da samun taimakonsa ga wannan nasara.

Lamido ta hannun ofishin yada labaransa ya ba da tabbacin samar da cigaba a yankin da zai wakilta, kamar yadda suka san shi mutum ne wanda yake kishinsu zai tabbatar sun samu romon dimukuradiyya waton ba zai ba su kunya ba.

Ibrahim Lamido ya godewa wannan karimci da aka yi mashi da fatar zai cigaba da samun goyon baya don tafiya tare cikin aminci da mutunci. 

Lamido na cikin Sanatoci biyu da jam'iyar APC ta samu a Sakkwato in da PDP ta samu ɗaya.