Gwamnatin Ahmed Aliyu ta jihar Sakkwato ta zargi jam’iyyar adawa ta PDP da yada karya da daukar nauyin rahotannin kage.
Gwamnatin ta ce PDP na fafutukar kawar da hankalin gwamnatin Ahmed Aliyu daga gudanar da ayyukan ci gaba da raya kasa da inganta rayuwar ‘yan Sakkwato.
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa babban sakataren yada labaran gwamnan Sakkwato, Abubakar Bawa, ya ce sun gano dabarun PDP na hana gwamnatinsu aiki a jihar.
Sanarwar da Abubakar Bawa ya fitar ta ce babu maganar bayar da kwangilar N30bn da ake zargin gwamnatin Sakkwato ta yi domin gina shinge waya a titunan jihar.
Gwamnatin ta ce abin da ke nan shi ne kwangilar N800m ce a sanya shinge a manyan titunan jihar wanda ake bukata saboda kare rayukan dalibai.
Gwamnatin Ahmed Aliyu ta jihar Sakkwato ta zargi jam’iyyar adawa ta PDP da yi mata bakin cikin ayyukan ci gaban da ake samu a jihar.





