Gaskiya APC ba za ta iya magance magance matsalolin Nijeriya ba - El-Rufai

Gaskiya APC ba za ta iya magance magance matsalolin Nijeriya ba - El-Rufai

Gaskiya APC ba za ta iya magance magance matsalolin Nijeriya ba - El-Rufai 

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana damuwar sa kan yadda jam’iyyar APC mai mulki ta kasa iya tunkarar kalubalen da kasar ke fuskanta.

Ya kuma zargi jam’iyya mai mulki da gwamnatin shugaba Bola Tinubu da yunkurin ruguza jam’iyyun adawa a kasar nan.

Yayin da ya ke bayyana ra’ayinsa game da haka jam’iyyun adawa ke ciki,  El-Rufai ya ce tsari da ingancin shugabanci a Najeriya na cikin halin ha'ula'i a ƙasar.

El-Rufai wanda da shi aka kafa jam’iyyar APC,  ya bayyana hakan a yayin wani taro kan karfafa dimokradiyya a Najeriya a Abuja a jiya Litinin.

Ya ce: “Ba na daukar APC a wata jam'iyya. Babu wani ɓangare na am’iyyar APC da ya yi taro tsawon shekaru biyu. Babu komi, babu kwamitin koli, babu komai. Sai dai bamu sani ba ko mutum daya ne ya mamaye komai” in ji shi.