Hukumar tace finafinai ta dakatar da mawaki da jarumai mata 2 

Hukumar tace finafinai ta dakatar da mawaki da jarumai mata 2 

Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta dakatar da mawakin Kannywood, Usman Sojaboy da wasu jarumai biyu, Shamsiyya Muhammad da Hasina Suzan daga shiga duk wasu harkoki na masana’antar fina-finan Hausa a jihar.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar dauke da sa hannun mai magana da yawunta, Abdullahi Sani Sulaiman a Kano a yau Litinin,  ta ce ta yanke hukuncin ne biyo bayan wani faifan bidiyo da aka yi ta yadawa inda ake zarginsu da aikata alfasha.

Sulaiman yace ayyukan sun sabawa addini da al'adar jihar Kano.

A cewarsa, hukumar ta dauki matakin ne bisa korafe-korafe da jama’a suka yi na cewa a dauki mataki kan yan Kannywood din.

Ya ce babban sakataren hukumar, Abba El-Mustapha, ya umurci sashin tantancewa da su tabbatar da cewa Sojaboy da jaruman biyu ba su shiga wani shiri na Kannywood ba.