Gwamnatin Kebbi ta baiwa matasa 'yan bangar siyasa 200 mukamin mataimaka na musamman ga Gwamna

Gwamnatin Kebbi ta baiwa matasa 'yan bangar siyasa 200 mukamin mataimaka na musamman ga Gwamna
 
A yunkurin Gwamnatin jihar Kebbi na mayar da matasa masu bangar siyasa su zama masu amfani a cikin al'umma Gwamna Nasir Idris ya baiwa matasa 200 da ke goyon bayan jam'iyar APC mukamin mataimaka na musamman gare shi tare da albashi a kowane wata. 
Shugaban jam'iyar a jiha Abubakar Muhammadu Kana Zuru ne ya gabatar da takaardar mukaman a sakatariyar jam'iya na jiha a ranar Alhamis data gabata.
Shugaban Kana Zuru ya bayyana wannan a matsayin wani bangare na cika alkwalin da Gwamna ya dauka na samarwa matasa masu harkar siyasa abin dogaro da kai domin ganin sun amfani al'umma da kansu.
"Gwamnan Kebbi ya cika alkawalin da ya dauka a lokacin yekuwar zabe da kashi 85. A matsayinsa na gogaggen shugaban fafutika, ya san girman gudanar da aiyukkan cigaba hakan ya sa ya sauya jiha tare yin gwamnatin hadin kai wadda ke tafiya tare da kowa, a cewarsa"
Shugaban matasa na jam'iyar Atiku Bio Zauro ya yi kira ga wadan da aka baiwa mukamin kar su baiwa gwamna kunya su zama masu bin doka da oda da kintsa kansu a duk sanda suke hulda da jama'a.
"Muna godewa Kauran Gwandu kan wannan karimci da ya yi na daukar daruruwan matasa daga cikin mu, su ba da ta su gudunmuwa a kowane wata kuma za a ba su dan ihisani," Zaura ya ce.
Malam Kalala daya daga cikin matsan da aka baiwa mukamin ya yi kira ga matasa su jingine duk wani  harkar bangar siyasa, su zama masu tarbiya da za a girmama.