Da ɗumi-ɗumi: “Ba Zan Bi Peter Obi Zuwa ADC Ba” — Gwamna Alex Otti

Da ɗumi-ɗumi: “Ba Zan Bi Peter Obi Zuwa ADC Ba” — Gwamna Alex Otti

Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana karara cewa ba shi da shirin ficewa daga jam’iyyar Labour Party, duk da matakin da Peter Obi ya ɗauka na barin jam’iyyar.

A cewarsa, ya shiga Labour Party tun kafin shigowar Peter Obi, don haka ba tare suka shigo ba.

“Peter Obi ya sanar da ni cewa zai bar jam’iyyar. Na sa ma shi albarka. Amma ni zan ci gaba da zama a Labour Party, domin in ci gaba da fafutukar ceto da sake gyara jam’iyyar,” in ji Otti.

Gwamnan ya ƙara da cewa:
“Jam’iyyar Labour Party ita ce ta kai ni ga mulki. Idan muka yi gwagwarmaya har ƙarshe muka samu mun gyara ta, daga nan ne za a iya tattauna wasu zaɓuɓɓuka.

 Amma a yanzu, ba zan koma kowace jam’iyya ba.”
Wannan bayani na zuwa ne yayin da ake rade-radin cewa Peter Obi na iya komawa African Democratic Congress (ADC).