Kauran Gwandu Zai Dora Daga Ingantaccen Mulkin Bagudu --- Aminu P. A 

Kauran Gwandu Zai Dora Daga Ingantaccen Mulkin Bagudu --- Aminu P. A 
 

Alhaji Aminu Danmusa, mataimaki na musamman ga zababben Gwamnan Jihar Kebbi, Nasiru Idris ya bayyana cewar Kauran Gwandu zai dora daga ingantaccen mulkin Abubakar  Atiku Bagudu tare da cika alkawullan da ya daukarwa al'ummar Jihar a yayin yekuwar neman zabe.

 
A tattaunawar da ya yi da manema labarai a Sakkwato, ranar Litinin, Aminu P.A. ya bayyana cewar zaben gaskiya da adalci da sahihin mulki nagari da Bagudu ya aiwatar ne suka baiwa Idris nasarar lashe zabe da gagarumar nasara a bisa ga yadda jama'a suka nuna masu halasci. 
 
Ya ce zababben Gwamnan yana da kwarewa da gogewar gudanar da mulki nagari don haka al'ummar Kebbi za su tabbatar cewar sun yi dacen Gwamna wanda zai shayar da su romon mulkin Dimokuradiyya ta yadda a nan gaba hatta 'yan adawa za su rungumi tafiyarsa ta gaskiya da adalci. 
 
"Hazikin gwarzon Gwamna, Bagudu, ya bunkasa sha'anin ilimi, aikin gona, inganta kiyon lafiya, shimfida hanyoyin mota, samar da ruwan sha da bunkasa tattalin arziki a tsayin shekaru takwas wanda Idris zai ci- gaba ta hanyar baiwa marada kunya."
 
A cewarsa yadda Bagudu ya bayar da fifiiko ga bunkasa yankunan karkara, karfafawa mata da matasa da samar da ayyukan yi da inganta sha'anin tsaro, ita ma sabuwar Gwamnatin Kebbi a karkashin jagorancin Idris za ta sauke nauyin da aka dora mata. 
 
Matashin dan siyasar ya kara da cewar "Zababben Gwamna Kauran Gwandu, haziki ne kuma jajirtacce wanda ya san ciki da wajen aiki da sanin dubaru da hanyoyin kawar da matsalolin al'umma da samar masu ci-gaba wanda a kan hakan ne Gwamna Bagudu a matsayinsa na mai hangen nesa, ya mika masa shugabancin wannan jiha mai albarka domin ya san zai iya yin duk aikin da aka bashi." Ya bayyana.
 
"Shugabancin da Kauran Gwandu ya yi a matsayin Shugaban Kungiyar Malamai ta Kasa (NUT) da zamansa Mataimakin Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ya nuna sadaukarwa, jajircewa da aiki tukuru wanda muke da tabbacin zai aiwatar da sama da hakan a Kebbi. 
 
Aminu P.A, wanda kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewar al'ummar Kebbi ba za su taba da- na- sanin zaben Kauran Gwandu a matsayin Gwamna ba. "Ko shakka babu Tinubu a matsayin Shugaban Kasa da Idris a matsayin Gwamna, Nijeriya da Jihar mu za su samu cikakkiyar nasara da amfana da mulkin Dimokuradiyya." Ya bayyana.