Kyakkyawar Manufar Sabon Gwamna ta ciyar da Sakkwato gaba zai tafi tare da kowa-----Alhaji Abba Tambuwal
Daga Nasiru Bello, Sakkwato.
Alhaji Abba Shehu Tambuwal daya daga cikin jigogin jam'iyar APC a jihar Sakkwato kuma yana cikin kwamitin karbar mulki da zababben Gwamnan jiha Alhaji Ahmad Aliyu kafa, ya yi magana kan gwamnatinsu da sauran batutuwa da suka shafi gwamnatinsu mai zuwa a zantawarsa da manema labarai, ga hirar kamar haka.
A matsayinka na jigo a jam'iyar APC ya kake kallon gwamnatin Ahmad Aliyu a gefen cigaban jihar Sakkwato?
Kamar yadda ka fadi ni jigo ne a jam'iyar APC ina kallon gwamnatin mu da za ta zo gwamnati ce mai albarka da mutane suka zaba cikin ikon Allah mai girma Ahmad Aliyu ya zama gwamnan Sakkwato, gwamnati ce da jama'a suka zaɓa domin fita daga ƙangin mulkin mallaka na jam'iyar PDP a jihar Sakkwato, mutane sun haɗu wuri ɗaya sun tsaya kai da fata sai an samar da cigaba, haƙar su ta cimma ruwa Ahmad Aliyu ya zama gwamna da gagarumin rinjaye, sai godiyar Allah. Ina kallon gwamnatin za ta zama irin ta Sarkin Yamman Sakkwato wurin sauraren jama'a da kulawa da su da yi masu aiki domin taimakonsu.
Dayawan masana na kallon gwamnatinku za ta fuskanci kalubale masu yawa musamman sha'anin bashi da za ta gada da matsalar tattalin arziki, mi za ku yi na ganin mutane ba su yi da sun sani ba?
Abu ne da muka san da shi tun kafin a zabe, mu ne Allah ya ba mu damar, mun san da badakar da aka kawo a Sakkwato wadda ta shafi tattalin arziki da jin dadi da walwala, aikin gwamnati a jiha kowa yasan yanda ya lalace mai girma zababben gwamna ya yi shiri da muke fatan Allah ya taimaka masa saboda kyakkyawar manufar da yake ga mutanen Sakkwato baki daya wadanda suka zabe shi da wadan da ba su zabe shi ba.
Jam'iyar adawa a jihar Sakkwato waton PDP ba ta nuna za ta ajiye adawa ta tafi tare da ku ba, kana ganin adawar ba za ta kawo maku cikas ba ga nasarorin da kuke son samu?
Jam'iyar adawa a Sakkwato ta kai karshe saboda mu ne adawa kuma mu ne muka amshi mulki da yardar Allah, su PDP ba za su iya adawa ba, tun a watan Junairun 2018 duk wanda yake ma'aikacin gwamnati a Sakkwato ba ya da dadin rai zuwa yanzu da aka kayar da PDP saboda duk wasu kudaden aiki an daina bayarwa tun daga asibitoci da wurin kashe gobara, gashi ana albashi a makare sai wani wata ya shiga a biya ma'aikata, yanzu haka ma'aikata na bin bashi albashin watan Fabarairu dana Maris ga Afirilu ya kare ba maganar albashin gaba daya, balle a yi maganar watan Mayu, ka ga wannan kalubale ne, yanda nasan sabon gwamna ya yi tsarinsa da zai sa mutane su yi rayuwarsu cikin sauki da walwala abin da zai sa a manta da gwamna mai barin gado Aminu Waziri Tambuwal ya sa mutane cikin wannan yanayin gaba daya, ka ko san in hakan ta tabbata ina maganar wata adawa.
Gwamnatin Aminu Tambuwal ta dauko aiyukka wasu an yi rabi wasu an kusa kammalawa wasu an fara ne matakin farko ku za ku yi kokarin kammala aiyukkan ko za ku fita batun su ne?
Kowa yasan gwamnatinmu mai son cigaba ce yanda ka san Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya gadi aiyukkan da Bafarawa ya soma ya kuma kammala su haka ma gwamnatin Ahmad Aliyu za ta kammala duk wasu aiyukka da ke da amfani ga jama'a da aka fara. Dubi asibitin kwararru ta jiha yanda aka yanke mata wutar lantarki ba injin bayar da wutar lantarki, asibiti na wari mai jinya da ma'aikaci da maras lafiya kowa a wahale cikin bacin rai, komi ya tsaya cak, jihar Sakkwato yanzu ne Allah zai karbe ta hannun mahara yanda ka san an yi garkuwa da mutane haka rayuwar 'yan jiha take babu bambanci da yaran matan Yawuri da aka kama amma yanzu an samu 'yanci da ikon Allah.
Ya zaka kwatanta jagorancinku da sauran gwamnonin Arewacin Nijeriya
Kamar yadda kasan 2007 zuwa 2015 a jagorancin Wamakko Sakkwato ba ta kishin wani aiki a wata jiha da ba a yi a Sakkwato ba sai dai a yi koyi da Sakkwato muma sai dai a yi koyi da mu. Ba za mu damu da duk wani kyalkyalin amsar mukamin kungiyoyi ba za a yi aiki ne tukuru a samar da ruwan sha da inganta rayuwar mutane da ma'aikatan gwamnati martabar aiki za ta dawo, muna cikin jihohi dake da dama ga gwamnatin tarayya domin APC a sama kamar nan jiha, mun kawo wa shugaban kasa kuri'un da suka dace a jihar DG na PDP.
Kana cikin mambobin kwamitin karbar mulki na APC ka gamsu da sauran mutanen kwamitin?
Duk mutanen da ka gani cikin kwamitin nan ya dace, ka duba shugaban kwamitin kwararre ne shekararsa 80 da wani abu yana rike da amana saboda ana son a yi gaskiya aka sanya shi, duk wanda aka sanya an san cancantarsa cikin mutanen nan guda 108. Rashin kaddamar da kwamitin gwamnati ba zai kawo mana ciks ga aiyukkanmu ba, muna aiki ba dare ba rana kan abubuwan da yakamata mu yi, za ka ji abin da zai faru da an kammala kafa kananan kwamitocinmu.
Wane irin albshir gare ka ga magoya bayan APC?
Albishir babba ne domin mun san Gwamnanmu dattijo ne mai magana ɗaya su sani alƙawalin da ya yi masu yana nan ba zai sauya ba duk wanda ya ba da gudunmuwa a tafiyar APC har aka samu nasarar kafa gwamnati lalle ba za a barshi baya ba zai samu romon dimukuraɗiyya ta hanyar adalci da bai kowa damar da ta dace da shi, abin da kawai ake buƙata mutane su sanya hakuri da bin komai a hankali, amma ina da tabbas duk wanda ya goyi bayan Sarkin Yamma da Amadu ba zai yi da ya sani ba, za a saka masa iya gwargwado.
Fatar ka ga mutanen Sakkwato da Nijeriya
Fatana Allah ya yi riƙo da hannayensa ya taimake shi ya cika buƙatar Sakkwatawa ta hanyar sauya abubuwan jiha ga alheri, ƙudurorinsa guda 9 da ya fitar harkar Ilmi da Lafiya da Ruwan Sha da harkar addini da tsaro da sauransu, matuƙar fatar Sabon Gwamna ta tabbbata lamurra za su gyaru domin shi Amadu duk wanda ya san shi ya san mutum ne mai son cigaban jiha, in ya shiga cikin lamari ba zai tsaya ba har sai ya tabbbatar an kammala abun cikin nasara. Ina fatar sanin da muka yi wa Gwamna kar ya sauya ya cigaba da riƙe mutane da amana ya kuma ƙara sanya biyayyarsa ga Sarkin Yamman Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a gaba lalle hakan zai ƙara kawo mana cigaba duk in da ka ganshi mutane ake yi wa hidima, kan haka lalle gwamnatin Amadu za ta kula da buƙatun Sakkwatawa, a cigaba da yi mata addu'a da an rantsar da shi za su ji kalamansa da aikinsa.