Babban Taron Ƙasa: APC Ta Faɗa Sabon Rikici
Gwamnonin APC sun yanke shawarar yin zama a wannan Lahadi domin tattauna halin da jam'iyar su take ciki. Ana ganin rikicin yanda za a raba muƙaman jam'iya zai sanya a ɗaga zaɓen shugabanin da aka tsara gudanarwa a watan Disamba zuwa watan Junairu don aiwatar da taron ƙasa. Rikicin raba muƙamai a yankunan ƙasa abu ne da zai iya kawowa jam'iyar na ƙasu a tun takarar zaɓen 2023.
Babban Taron Ƙasa: APC Ta Faɗa Sabon Rikici
managarciya