Daga Abdullahi Alhassan, Kaduna
Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalissar Dattawa ta kasa dake Abuja, haka kuma dan takarar kujerar Gwamnan jihar Kaduna a karkashin jami'yar APC sanata Uba Sani,ya ce duk nasarar daya samu a matsayin sa na sanata mai wakiltar Al'ummar Kaduna ta tsakiya ya biyo bayan gudumawar da Bello El-rufa'i ne ya bashi a cewar Sanatan.
Sanata Uba Sani yana wannan maganar ce yayin kaddamar da Kwamitin yakin neman zaben Bello El-rufa'i ne amatsayin dan takarar kujerar Majalissar wakilai ta tarayya kasa dake Abuja a Kaduna, inda ya Kara da cewa lalle Bello El-rufa'i yaro ne haziki mai aiki tukuru da ya taimaka min mutuka wajen gabatar da kudurori, ya yin aikin da nayi dashi a matsayin Shugaban ma'aikata na a matsayin na -na sanata.
Ya kuma Kara da cewa ni ne na ce masa da ya fito ya nemi Kujerar Majalissar wakilai ta tarayya ta Kaduna na Arewa a Majalissar wakilai dake Abuja,ka san cewar sa matashi kuma haziki mai ganin mutumcin manyan,wanda lna fatan in ya samu za'a samu wakilci da zai maida hankali kan Gina rayuwan Mata da Matasa na wan nan yakin.
Ha kazalika dan takarar kujerar Gwamnan jihar Kaduna na ya yi amfani da wan nan damar wajen gabatar da sauran yan takarar kujerar Majalissar jihar Kaduna,inda yace"ga Naziru Abubakar nan da Aminun Auntie,Yara ne hazikai samu mutumci da muke fatan zasu samar da wakilci nagari a majalissar jihar Kaduna,saboda haka don Allah abasu dama inji dan takarar Gwamnan.
Shi kuwa a nashi jawabin darectan yakin neman zaben Bello El-rufa'i,Honarabul Aliyu Sani Bakori ,cewa ya yi lokaci ya yi da samu hadda kai mu wajan ganin mun samu nasarar wan nan zaben, saboda haka lna amfani da wan nan dama don lnyi roko ga duk wan aka batawa rai da yayi hakuri,
"Saboda haka zamu fita ne mu roki jama'a cewa su bamu dama kan kudurori da manifufi da muke da shi na ganin an bamu wan nan damar na wakiltar su a majalissar kasa kuma muna rokon su da su zabi Jam'iyyar A P C tun daga sama har kasa haka kuma daga kasa har sama.
Tun da fari ,dan takarar kujerar Majalissar wakilai din wato Bello El-rufa'i,farawa ya yi da godewa jama'ar jihar Kaduna kan goyon bayan da suka bawa mahaifinsa, inda yayi kira da jama'ar da shima su bashi irin wan nan damar ta hanyar zaben sa don ya wakilce su a majalissar tarayya ta kasa dake Abuja.
Bello El-rufa'i,ya Kara da cewa,lna fatan samar da wakilci nagari,wanda za'a ce gwamma da akayi,haka kuma zan bawa Mata da Matasa mutukar muhimmamci kasan cewar nima matashi ne, don kuwa duk Al'ummar da take sun cigaba sai ta kula da Mata da Matasa ta hanyar samar musu da abubuwan cigaba,da zai maida hankali wajen samar musu da Jari da kuma Sana'oi yin don dogaro da Kai.