MURIC ta sake zargin Gwamnatin Sokoto na yunkurin karya Sarkin musulmi

MURIC ta sake zargin Gwamnatin Sokoto na yunkurin karya Sarkin musulmi

 

Duk da Gwamna Ahmed Aliyu ya fito ya karyata lamarin, ƙungiyar MURIC ta nanata cewa har yanzun gwamnan na shirin tsige Sarkin Musulmi. 

Ƙungiyar MURIC mai fafutukar kare haƙkin al'ummar Musulmi a Najeriya ta jaddada cewa gwamnatin jihar Sakkwato na nan kan bakarta na sauke Sultan. 
Babban darektan MURIC na ƙasa, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. 
Ya ce kudirin garambawul ga dokar masarautar Sakkwato, wanda ya tsallake karatu na farko dana biyu zai rage karfin ikon Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar.
Majalisa ta tsiri gyaran dokar ne a daidai lokacin da kungiyar MURIC ta yi zargin cewa Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu na shirin tsige Sarkin Musulmi. 
Bayan haka kuma aka ji mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima na rokon Gwamna Aliyu ya bayar da kariya ga Sarkin Musulmi maimakon tsige shi. 
Sai dai gwamnatin Sakkwato ta fito ta musanta zargin, inda ta roki Shettima ya riƙa bin diddigi da tabbatar da gaskiya kafin ya yi magana kan batutuwan da suka shafi ƙasa, Vanguard ta kawo.