Maganin Mata Na Musulunci

Bayan haka, hakika ita mace kowa ya san wata karkatacciyar halitta ce wadda aka halitta da raunataccen kashi, tare da ɗimuwar tunani. Mace raunanniya ce akan komai na ta,tun kan yanayin jikinta halayen ta da dabi'unta. Akan haka ne ba ta da wuyar shan kai a cikin kowa ce harka.

Maganin Mata Na Musulunci
Maganin Mata Na Musulunci
Maganin Mata Na Musulunci

Bissimillahi rahmani rahim.
Ina farawa da sunan Allah,ubangijin sammai da kassai. Ubangiji kai ne wanda ya halitta ma maza mataye daga kawunansu, domin su sami nutsuwa izuwa gare su. Kai ne wanda ka sanya soyayya da jinkai a tsakanin su.
Bayan haka, hakika ita mace kowa ya san wata karkatacciyar halitta ce wadda aka halitta da raunataccen kashi, tare da ɗimuwar tunani. Mace raunanniya ce akan komai na ta,tun kan yanayin jikinta halayen ta da dabi'unta. Akan haka ne ba ta da wuyar shan kai a cikin kowa ce harka.
   Sai dai acikin taɓarɓarewar tarbiya ta 'ya mace abubuwa uku sun fi taka rawa wurin saurin lalacewar tarbiyar ta. Duba da yadda kullum al'amurra ke kara lalacewa mata a wannan ƙarnin.
SOYAYYA:kowa ya san soyayya wata aba ce mai ruɗarwa da makantar idanu tare da kurmantar da kunnuwa da dimauta tunani musamman na 'ya mace mai gajeren tunani da rauni na zahiri ko na baɗini.
  Mata da  dama suna shiga cikin wani ciwo ko kamuwa da cuta mai kama da taɓin hankali,wanda a zahiri zaka gansu kamar mahaukatan na gaskiya.
'Ya mace na shiga cikin mummunan hali yayin da ta fada soyayya,saboda mafi akasarin mata lokacin da suka faɗa a cikin wannan cakwakiyar ta soyayya,su kan shiga ne gaba gaɗi,batare da tsayin yin wani gwaggwaɓan tunani akan  wannan harƙallar da aka ƙulla da su.
Da yawan mata suna daukar yaren soyayya tamkar wani wahayi ne ake saukar musu a zukatan su,wanda zai kasance wajibci wurin yin imani da wannan wahayin,tare da cika umurnin mai saƙon.
Karancin tunani mace da rashin isassun sinadaran hangen nesa,ya janwo ma mace tabarbarewar tarbiyar da ta samu agaban iyayen ta,da wadda ita kanta ta yi fafutukar nema don ganin ita ma ta kasance mace wadda al'umma ke muradin samu acikin wannan duniyar ta AL-MALIKKU.
Soyayya ta taka muhimmiyar rawa wurin ruguje tarbiyar da watse ainihin tubalin ginin da musulunci ya gina 'ya mace dashi!
Duk da soyayya iri biyu ce,akwai SOYAYYAR GASKIYA,DA SOYYAYAR ƘARYA.
Acikin wannan lokacin, soyayyar ƙarya ita ce tafi komai yawa da sauƙi ga maza zuwa ga mata, kodayake ana samun masu cewa kowane ɓangare ana samun mayaudara tsakanin namiji da mace.
Sai dai wannan ba maganar yaudara ce ta sashe da sashe, magana ce akan mahangar mace acikin soyayya.
Daga lokacin da mace ta samu kanta acikin kungurumin dajin soyayya,idan bata dace ba, daga sannna ne mafarin shigarta damuwa da tabarbarewar tarbiya, rusa gida, da gadarwa 'ya'ya da jikoki abin faɗe a gari.
Muyi nazari akan wannan
Ayau da komai ya lalace, duniyar mata ta ƙara fadada yayin da farashin matan kullum daɗa faɗuwa yake yi warwas a ƙasa! Amma hakan bai sanya mace tunani mine ne makomata acikin wannan tafiyar, shin idan na saka hannun jari acikin wannan harƙallla zan sami riba ko zan faɗi?
Tukunna ma da wa zan yi wannan harkallar?
Wannan shi ne abin da ya kamata mace ta fara tunani kafin ta tsunduma cikin tafkin da zai ƙafe mata kafin ta ƙare wanka.
Lokaci ya zo da canje-canje masu yawa,wanda wadannan canje-canje ci baya ne ga rayuwar mace.
Iftila'ai sun karu da yawa agidanjen mu sanadiyar bahaguwar soyayya,yayin da kullum gidan karuwai ke ƙara samun baƙin mata a sanadin gurɓatacciyar soyayya. Haka kuma kullum ana haihuwar jarirai sama da 10 sandiyar rashin dacewa da soyayyar gaskiya.
Rubutu ne aka yi a matsayin maganin mata na musulunci da zai an karar da su rayuwar da suke ciki domin gyara tafiyarsu ta gama a cikin wannan bahagon zamani.
Zan ci gaba
ZAINAB ALIYU SIFAWA.