2027: Kungiyar ATT Ta Rena Arewa ne Ko Tana yi wa Tinubu Kamfe?

2027: Kungiyar ATT Ta Rena Arewa ne Ko Tana yi wa Tinubu Kamfe?

Kungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta bayyana cewa babu wani dalili da zai hana yankin Arewa goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027. Kungiyar ATT ta ce Arewa za ta goyi bayan Shugaba Tinubu, duba da ci gaban da gwamnatinsa ta kawo a fannin tsaro da ababen more rayuwa a yankin. 

Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jagoran kungiyar, Muhammad Alhaji Yakubu, ya fitar a ranar Laraba, 30 ga watan Yulin 2025. 
Muhammad Alhaji Yakubu ya ce mayar da hankalin da Shugaba Tinubu ke yi wajen ci gaban yankin Arewa ya haifar da sakamako mai kyau, wanda ya cancanci ci gaba da goyon bayansa. "Arewa Think Tank na kira ga mutanen Arewa da su tsaya tsayin daka tare da shugaban kasa kuma su sake zaɓensa a 2027." "Dole ne mu faɗa wa kanmu gaskiyar magana cewa a halin yanzu, Arewa ba ta buƙatar mulki, sai dai ababen more rayuwa da ci gaban ɗan Adam wanda Shugaba Tinubu ke ci gaba da kawo wa mutanenmu." 
Wannan sanarwar na zuwa ne bayan wani taron shugabanni da aka gudanar a Kaduna, inda shugabannin siyasa daga Arewa suka yi nazari kan mulkin Tinubu. Yayin da wasu ke nuna damuwa da talauci da matsalolin tsaro, wasu kuwa sun yaba da wasu manyan shirye-shiryen gwamnatin tarayya da ke mayar da hankali kan Arewa.