Zaɓen Shugabannin Jam'iya na Ƙananan Hukumomi ya ƙara ta'azzara rikicin da ke jam'iya mai mulki ta APC a Jihar Zamfara in da lamarin ya kara kazancewa abin da ake kallo dakyar wani bangare bai kori wani a jam'iyar ba.
Rahotanni sun baiyana cewa zaɓen ya sanya APC ta rabe gida uku, inda kowanne ɓangare ke iƙirarin cewa shi ne halastacce a shugaba a jam'iyar.
Ɓangarori ukun su ne na gwamna, Bello Muhammad Matawalle, wanda tsohon gwamnan jihar, Ahmed Yarima ke goyawa baya, sai ɓangaren tsohon gwamna, Abdul'aziz Yari sai kuma na Sanata Kabiru Marafa wanda suke a tare su kuma.
Da ya ke jawabi a jiya Asabar, Matawalle ya yi kira ga duka ɓangarorin da su maida wuƙarsu kube su dawo a haɗe kai domin ciyar da jihar gaba.
Matawalle ya yi wannan kira ne a Sakateriyar Ƙaramar Hukumar Maradun, inda ya ke ganawa da wakilan zaɓen na ɓangarensa bayan ya yi zaɓe, a mahaifarsa.
"Ni har yanzu a gani na APC ɗaya ce a jihar nan tunda har yanzu babu wata kotu ko uwar jam'iya da ta ce a dakatar da zaɓen shugabannin jam'iya da aka shirya gudanarwa.
"Kasancewar babu wani umarni daga kotu ko uwar jam'iya ta ƙasa kan a dakatar da zaɓen jam'iyar, to hakan ya nuna cewa lallai zaben halastacce ne," in ji Matawalle.
Gwamnan ya kuma zargi wasu daga cikin 'yan jam'iya da yaudarar wasu, ciki har da masu sukar shugabannin jam'iyar a jihar dama ƙasa baki ɗaya.
APC a Zamfara ta tsunduma cikin rikici tun bayan da gwamna Matawalle ya koma cikin jam'iyar, in da wadanda ya sama a cikinta ba su amince da jagorancinsa ba.