Sanata Wamakko Ya Yi Kira Ga Ɗalibban Nijeriya Su Riƙe Tarbiyarsu
Shugaban kwamitin tsaro a majalisar dattawa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya shawarci ɗalibban Nijeriya su jefar da duk wasu abubuwa da za su taɓa mutuncinsu a lokacin da suke karatunsu.
Sanata Wamakko ya faɗi haka a lokacin da yake karɓar shugaban ƙunguyar ɗalibbai na jami'ar Usman Ɗanfodiyo dake riƙon ƙwarya a lokacin da suka ziyarce shi a gidansa dake Sakkwato.
Sanata ya shawarce su kan mayar da hankali a karatunsu haka kuma koyaushe su zama masu gaskiya don samarwa Nijeriya cigaba a jagoranci na gaba.
Tsohon Gwamnan na Sakkwato ya tabbatar da zai cigaba da taimakon matasa a kan harkokin ilminsu.
Da farko Shugaban ɗalibban Malam Shamsudden Umar ya ce sun kawo ziyarar ne akan ƙoƙarin Sanata ga harkokin ilmi.
Ya bayyana Sanata a matsayin uban matasa dake ƙoƙarin inganta rayuwarsu a cikin al'umma.
Shugaban ɗalibban ya gabatar da karramawa ga Sanata kan ƙokarinsa kan cigaban ilmi.
A bayanin da mai baiwa Sanata Shawara kan yada labarai Hassan Sahabi Sanyinnawal, ya fitar wanda Managarciya ta samu ne aka samu bayani.