An ƙone wata mata da ɗanta a  Kano 

An ƙone wata mata da ɗanta a  Kano 

Mazauna unguwar Sheka Sabuwar Gandu da ke cikin birnin Kano sun shiga firgici a ranar Lahadi bayan kisan wata mata mai juna biyu da ɗanta mai watanni 18 da wasu da ba a san ko su waye ba suka aikata.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a yammacin ranar Asabar, lokacin da mijin matar ya dawo daga wurin aiki da misalin ƙarfe 8 na dare, inda ya tarar da ƙofar gidansa a kulle daga waje.

Rahotanni sun ce mijin ya balle ƙofar, sannan ya shiga ya ga gawar matarsa da ɗansu a kwance, inda a ka kai musu hari tare da ƙona su.

Wani jagoran al’umma, Ahmad Sani, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai kokawa kan rashin isasshen tsaro a yankin.

Sani ya ce mazauna yankin sun haɗa kai suka gina ofishin ‘yansanda a unguwar, amma har yanzu hukumomi ba su tura jami’ai domin kula da wurin ba.

Ya yi kira ga Kwamishinan ‘Yanwanda na Jihar Kano, Ibrahim Bakori, da ya gaggauta tura jami’ai zuwa ofishin domin ƙarfafa tsaro da kuma hana sake aukuwar irin wannan hari.

Da aka tuntubi Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yansanda a Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Haruna ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.