A karon farko tun kafa jihar Zamfara, ba'a taba rantsar da makaraban gwamnati irin wanda ya gudana a yau din nan ba, a fadar gwamnatin jihar.
Gwamnan jihar ta Zamfara Bello Muhammed Matawalle ya tsaya kai da fata cewa duk wanda aka ba mukamin siyasa kafin rantsar da shi sai ya rantse da Alkur'ani mai girma cewa ba shida sa hannu, cikin matsalar tsaron jihar.
A wajen rantsuwar kowanen su ya rantse ba shida hannu, ko kuma idan akayi ta'addanci zaiji dadi, ko ingiza wasu domin su yi wannan ta'ddan cin.
Wannan manuniya ce na kokarin da gwamnan ke yi na jawo mutanen kirki wadanda na san yakamata masu tausayin jama'a a gwamnatin sa.
Wayanda dai aka rantsar a mukamai daban daban sun hada da sabon sakataren gwamnatin Alhaji Kabiru Balarabe, da kuma sabon shugaban ma'aikata, Alhaji Kabiru Mohammed, da kwamishinoni goma sha takwas 18, da masu bada shawara na musamman su goma sha daya 11, da wasu sakatarorin din din din.
Da yake jawabi wajen rantsuwar kama aikin wayannan mukarraban nasa, gwamnan yace,
"Gwamnatin mu bazata taba yarda da duk wani wanda zai mayar muna da hannun Agogo baya ba game da sha'anin tsaro. "Yan ta'addan nan na shan wahala a a cikin dazukan da suke, kuma ina bada tabbacin cewa nan bada jimawa ba za'a kara samun saukin su.
Ya karayin bayani bisa ga irin nasarorin da aka samu, biyowa bayan matakan da gwamnati ta dauka kan sha'anin tsaro, yace yanzu haka yan ta'addan suna gudu da kaifin kafar su suna barin jihar zamfara, bayan da aka kashe daruruwan su, kuma aka kama wasun su da rai, da kuma masu hadaka da yan ta'addan.
" Mun shirya taimaka wa mutanen mu da abun masarufi domin mu rage masu radadin da suke ji sakamakon wannan matakin na tsaro da muka dauka.
"Muna kara kira ga jama'ar wannan jihar da su kara hakuri, bisa ga wannan aikin da mukeyi" inji Matawalle.
Daga Aminu Abdullahi Gusau.