Nasarar Da Sojoji Suka Samu A Rabah Abin Yabawa Ne---Ibrahim Lamido

Nasarar Da Sojoji Suka Samu A Rabah Abin Yabawa Ne---Ibrahim Lamido

 

Dan takarar Sanata a gabascin Sakkwato cikin  jam'iyar APC Alhaji Ibrahim Lamido ya yabawa kokarin rundunar Sojan Nijeriya da ta kai dauki ga mutane, in da aka samu nasarar kashe 'yan ta'adda 16 bayan jikkata wasu da dama a yankin karamar hukumar Rabah.

Lamido ya nuna gamsuwarsa da cewa matukar gwamnti ta tashi tsaye musamman ta jiha za ta iya magance matsalar tsaro cikin kankanen lokaci.
Ya ce wannan kicibis da soja suka yi da 'yan bindiga da za su samu kwarin guiwa a wurin gwamnatin jiha aiyukkansu za su wuce haka.
Ya yi kira ga mutane su daina siyasantar da harkar tsaro hakan ke sanya mai laifi baya ganin laifinsa, balle ma ya gyara don samar da cigaban jiha ta haujin tsaro.
Lamido ya nuna takaicinsa kan yadda gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal  ke kin baiwa tsaro muhimmanci, a ce a samu irin wannan nasarar a jiha, da faruwar lamarin a kasa ganin gwamna ya je wurin domin ganin nasarar da aka samu domin duba hanyoyin karfafa sojoji a wannan fadan da suke yi, hakan ke nuna tashin hankalin da mutanen gabascin Sakkwato suke ciki ba shi ne damuwarsa ba.
Lamido ya tabbatar da cewa matukar Allah ya sa ya samu nasarar a zaben 2023 ba zai yi kasa a guiwa ba sai mutanen gabascin Sakkwato da jiha baki daya sun samu zaman lafiya da wadatuwar tsaro.