Jami'an Tsaro Sun Sake Kashe Tantirin Jagoran 'Yan Bindiga a Sokoto

Jami'an Tsaro Sun Sake Kashe Tantirin Jagoran 'Yan Bindiga a Sokoto

 
Gamayyar jami’an tsaro sun kashe wani shahararren jagoran 'yan bindiga mai suna Kachalla Na’Allah a jihar Sokoto. Jami'an tsaron sun kashe Kachalla Na'Allah ne a wani gagarumin farmaki da suka kai a karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto, lamarin da ya sake raunana cibiyoyin ’yan bindigan da ke addabar yankin. 
Jaridar Vanguard ta ce wata majiya mai tushe daga hukumomin tsaro ta tabbatar da cewa an harbe Kachalla Na’Allah ne har lahira a ranar Juma’a, 12 ga watan Disamban 2025. 
An harbe tantirin jagoran 'yan bindigan ne yayin da jami’an tsaro suka tare shi a tsakanin kauyukan Girnashe da Kuka Tara, a gundumar Tsabre ta karamar hukumar Isa. 
Majiyar ta bayyana cewa farmakin ya gudana ne ta hannun rundunar hadin gwiwa ta ’yan sanda na Mobile Police da jami’an rundunar tsaron al'umma, tare da goyon bayan sojojin Najeriya, rahoton gazettengr ya tabbatar da labarin. 
Aikin hadin gwiwar da jami'an tsaron suka yi ya kai ga samunn nasarar kashe babban jagoran na ’yan bindiga wanda ya addabi mutane. 
An bayyana cewa Kachalla Na’Allah ɗan uwan shahararren jagoran ’yan bindiga ne, Ibrahim Chimmo, wanda ake zargin yana buya a yankin Dajin Sububu. 
Majiyar ta ce wannan nasara na nuni da gagarumin ci gaba wajen tarwatsa shugabanci da tsarin aiki na kungiyoyin ’yan bindiga a jihar Sokoto. 
Wannan lamari na zuwa ne ’yan kwanaki kaɗan bayan dakarun runduna ta 8 ta sojojin Najeriya sun kashe wani sanannen jagoran ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, a karamar hukumar Sabon Birni. 
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan tantiran 'yan bindiga a jihar Sokoto. Dakarun sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun samu nasarar kashe ’yan bindiga 11 tare da kwato manyan makamai da dama daga hannunsu. 
Rundunar ta ce bayan ta samu sahihan bayanan sirri, tawagar jami'anta sun kaddamar da kwanton bauna mai tsari, inda aka yi artabu mai zafi da ’yan bindigan, lamarin da ya yi sanadiyyar hallaka wasu daga cikinsu.