Iyaye Mata: Yaushe Ne Gwamnatin Sakkwato Za Ta Bari Su Ci Amfanin Motocin Alfarmar Da Aka Saya Musu?
Wasu mutane na ganin tun farko gwamnti ta yi ragon azanci don bai kamata ta sayi irin wadan nan motoci a yi sufuri
Sama da wata uku kenan a yanzu da kaddamar da motocin sufuri na alfarma da ke da tsadar gaske da aka sanyawa sunan IYAYE MATA da Gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu Sokoto ya sayo, a yanzu mutane a birnin jiha na kokawa kan rashin sanin dalilin da ya hana gwamnati ta bar motocin su rika zagayawa a cikin al’umma kan manufar da aka sayo su saboda ita.
Wasu mutane na ganin ba amfani gwamnati ta kaddamar da motocin bayan ta san bata shirya barin motocin su zagaya ba, domin ragewa mutane radadin wahalar da aka shiga bayan cire tallafin man fetur.
Wasu mutane na ganin tun farko gwamnti ta yi ragon azanci don bai kamata ta sayi irin wadan nan motoci a yi sufuri da su ba a jihar da ke dimbin matsalolin rashin tsaro da talauci da rashin ingantattar kiyon lafiya.
Tsohon Mai baiwa Gwamna shawara Alhaji Kabiru Aliyu a lokacin da yake magana kan motocin ya roki gwamnatin jiha ta fito ta gaya wa mutane hakikanin lamari kan abin da ya shafi motocin.
A cewarsa "gwamnati ke da alhakin sanar da jama'a dalilin da ya sa ba a fara sufuri da motocin ba."
A binciken da aka yi motocin guda 20 suna ajiye a fadar gwamnatin jiha in da rana ke ta bugunsu ba tare da sanin makomar lokacin da za a dauke su ba.
Ko mine ne dai yakamata gwamnati ta yi karin haske kan lamarin domin mutane nason sanin makomar motocin ganin yanda suke da tsada gara a yi abu Mai tasiri.