Gwamnatin Buhari Ta Shawarci ’Yan Najeriya Su Gaggauta Goge Wasu Manhajojin Na’ura A Wayoyinsu

Gwamnatin Buhari Ta Shawarci ’Yan Najeriya Su Gaggauta Goge Wasu Manhajojin Na’ura A Wayoyinsu


Hukumar Kula da Harkokin Sadarwar ta Najeriya ta gano wasu abubuwan da ka iya kawo tsaiko ga 'ya kasa a kan manhajar Google Chrome. 

A cewar hukumar, irin wadannan manhajoji na bin diddigin duk wasu shafuka da mai amfani dasu ke bi. NCC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafin yanar gizo, wanda Legit.ng ta gani.
Manhajojin guda biyar da NCC ta ce 'yan kasa  su gujewa McAfee Mobile 
Netflix Party/Netflix Party 2
 Full Page Screenshot Capture Screenshotting 
FlipShope Price Tracker Extension 
AutoBuy Flash Sales 
NCC ta yi gargadin cewa, duk da akwai mutum sama da miliyan 1.4 dake amfani da manhajojin, duk da haka akwai hadarori da ke tattare dasu idan ba a kula ba. 
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, NCC ta ce akwai manhajojhi da yawa da Google suka cire a ma'ajiyar manhajoji Web Store, to amma abu ne mai wahala iya tsaftace kafar ta yanar gizo. 
A bangare guda, NCC ta shawarci masu amfani da wayoyin hannu da sauran abubuwan zamani da su ke karatun ta natsu kafin sauke manhaja a na'ur'rinsu. 
Ana amfani da Chrome Extensions a na'urorin teburi da na tafi d agidanta, kana ana amfani da irin manhajojin da NCC ke gargadi a kai a wayoyin hannu.