Gwamnatina  Ba Ta Samun Kururutawa a Wurin Manema Labarai----Tambuwal

Gwamnatina  Ba Ta Samun Kururutawa a Wurin Manema Labarai----Tambuwal


Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya koka kan yadda manema labarai a jihar Sakkwato ba sa kururuta aiyukkan da yake yi a jiha kamar yadda ya kamata.
Tambuwal ya nemi manema labarai su riƙa sanar da mutane aiyukkan da yake gabatarwa mutanen jiha na cigaba.
"Kamfe ya soma muna son ku sanar da mutanen Sakkwato a yi siyasa ba da gaba ba, ba mu aminta matasa su dauki makami ba, magoya bayanmu sun aminta da hakan, abin da muke so ne domin kara gyara tarbiyar matasanmu, muna iyakar kokarinmu a tabbatar da haka," a cewarsa.
Ya ce suna kan ƙoƙari kan matsalar tsaro da ake da shi a Sabon Birni da Isah da Goronyo da wani gefen Illela.
Tambuwal ya yaba abin da ya faru a garin Dange na fitowar mutane sosai a wurin ƙaddamar da yekuwar zaɓen gwamna a PDP  ya ce  a baya ba a samu yawan mutane sun fito kamar  wannan ba.
Gwamna Tambuwal kan wanda yake son ya gade shi ya ce "Malam zai cigaba da in da muka tsaya a wurin  samar da zaman lafiya  a jiha, da kawo cigaba  mun san irin yanda yake a tsantseninsa a harkokin rayuwa.
"Ba mu siyasar cin zarafi don har yanzu sakataren APC ma'aikacin gwamnati ne ba mu musguna masa ba.
"Mun yi aiki da 'yan majalisar APC cikin mutuntawa, na yaba masu kan fahimtar juna, siyasa abu ne na kawo cigaba a jiha ba samar ci baya ba. Muna son a ƙara ɗaukar aikin da gwamnati ke yi cikin adalci," a cewar Tambuwal.
Gwamna Tambuwal ya ce sai G-5 sun yi matsaya ta ƙarshe sannan ne jam'iya za ta yi magana kan abin da suka cimma.