Gwamna Buni Ya Sanya Hannun Ga Kasafin Kudin 2023 Na Naira Biliyan 163.5

Gwamna Buni Ya Sanya Hannun Ga Kasafin Kudin 2023 Na Naira Biliyan 163.5
 

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

 

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya rattaba hannu a kan kasafin kudin shekarar 2023 na Naira biliyan 163.5, biyo bayan samun amincewar zauren Majalisar dokokin jihar. 

 
Taron rattaba hannu kan kudirin kasafin shekarar 2023 ya gudana ne a babban dakin taron gidan gwamnatin jihar da WAWA Hall dake Damaturu.
 
Gwamna Mai Mala Buni ya ce anyi wa kasafin kudin 2023 da taken: “Kasafin kudi don ci gaba da ayyukan da aka fara, dora ginshikin bunkasa fasalin tattalin arziki”, wanda zai mayar da hankali ne kan kammala manyan ayyuka a fadin jihar.
 
Ya bayyana cewa kasafin kudin shekarar 2023 wanda ya gabatarwa da zauren majalisar dokokin jihar a watan da ya gabata, na jimkar kudi naira biliyan 163,155,366,000.
 
Gwamnan ya bayyana cewa a bisa sanya tabaraun hangen nesa, majalisar dokokin jihar ta yi wasu gyare-gyare inda ta rage adadin kasafin kudin zuwa ₦163,005,366,000.
 
Ya ci gaba da cewa kasafin ya kunshi bangaren ayyukan gwamnati na yau da kullum da manyan ayyuka na shekarar 2023 wanda suka doshi naira biliyan 87.8. da kuma naira biliyan 75.1 a takaice.
 
Gwamna Buni ya yi nuni da cewa, amincewa da kasafin kudin shekarar 2023 da majalisar dokokin jihar ta yi cikin lokaci ya na nuni irin kyakkyawar alakar aiki dake tsakanin bangarorin gwamnati biyu a jihar, abin a yaba ne kuma zai taimaki jihar wajen bunkasa da ci gaba.
 
“Wanda hakan zai taimaka jihar ta kammala sauran dukkan ayyukan da muke aiwatarwa kamar filin jirgin sama da ke Damaturu (International Cargo), Kasuwannin Zamani da tashar manyan motoci (Trailer Park) a Potiskum domin bunkasa tattalin arziki da kudaden shiga da jihar ke samu a cikin gida."
 
“Gwamnatin jiharmu za ta bullo da sabbin hanyoyi don kara samar da guraben ayyukan yi ga al'umma don samun dogaro da kai a tsakanin matasa."
 
"Ina so in yi kira ga dukkan masu rike da mukaman gwamnati, ma'aikatan gwamnati, da 'yan kwangila da su ci gaba da kiyaye gaskiya, rikon amana, bin ka'ida da kuma tsarin tafiyar kudi wajen aiwatar da kasafin kudin 2023." In ji Gwamnan.